التكاثر

At-Takaathur

Competition · Surah 102 · Ayahs: 8 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. أَلۡهَىٰكُمُ ٱلتَّكَاثُرُ

    Open ayah 102:1

    Alfahari da yawan (\'ya\'ya da dukiya) ya shagaltar da ku.

  2. حَتَّىٰ زُرۡتُمُ ٱلۡمَقَابِرَ

    Open ayah 102:2

    Har kuka (mutu kuka) ziyarci ƙaburbura.

  3. كَلَّا سَوۡفَ تَعۡلَمُونَ

    Open ayah 102:3

    A\'aha! (haka bai kamace ku ba) da sannu za ku sani.

  4. ثُمَّ كَلَّا سَوۡفَ تَعۡلَمُونَ

    Open ayah 102:4

    Sannan a\'aha, da sannu za ku sani.

  5. كَلَّا لَوۡ تَعۡلَمُونَ عِلۡمَ ٱلۡيَقِينِ

    Open ayah 102:5

    Tabbas da za ku yi sani, sani na sakankancewa.

  6. لَتَرَوُنَّ ٱلۡجَحِيمَ

    Open ayah 102:6

    Tabbas haƙiƙa za ku ga wutar Jahimu.

  7. ثُمَّ لَتَرَوُنَّهَا عَيۡنَ ٱلۡيَقِينِ

    Open ayah 102:7

    Sannan tabbas haƙiƙa za ku gan ta gani da ido na sakankancewa.

  8. ثُمَّ لَتُسۡـَٔلُنَّ يَوۡمَئِذٍ عَنِ ٱلنَّعِيمِ

    Open ayah 102:8

    Sannan kuma tabbas lalle za a tambaye ku a wannan ranar game da ni’imomin (da kuka mora a duniya). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da tsawatar wa mutane game da yadda alfahari da tara ‘ya’ya da dukiya ya shagaltar da su daga bin Allah (Mai tsarki da daukaka), suka doge a kan haka har sai da suka mutu suka shiga ƙaburburansu. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ba talauci nake ji muku tsoro ba; ina ji muku tsoron alfahari da tara dukiya; ba kuma kuskure nake ji muku tsoro ba, ina ji muku tsoron ganganci ne.” [Ahmad #8074 da Ibn Hibban #3222 da Hakim #3970]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna musu cewa, bai dace a ce irin wannan mummunar ɗabi’a ta alfahari da tarin dukiya ko ‘ya’ya ta ɗauke musu hankali ba har su kai ga barin ɗa’ar Allah, domin ba da jimawa ba za su san rashin amfanin abin da suka yi. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu da cewa, tabbas da sun san za a tashe su a gaban Allah, ya yi musu hisabi da sakayya a kan ayyukansu, to da lalle ba su shagala da tara dukiya da alfahari da ‘ya’ya ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, lalle babu makawa sai sun ga wuta a ranar alƙiyama, gani kuma na sakankancewa wanda babu kokwanto ko kaɗan a cikinsa. Ya kuma ya tabbatar musu cewa, lalle ba makawa sai an tambaye su a ranar alƙiyama game da ni’imomin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu, kamar ni’imar lafiya ko ta wadata da makamantansu. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Bawa yakan ce: “\'Dukiyata, dukiyata\', alhali abu uku ne kawai nasa a cikin dukiyarsa; abin da ya ci ya ƙarar, da tufar da ya sa ya kashe, da abin da ya bayar sadaka ya yi wa kansa ajiya. Duk abin da ba waɗannan ba, to zai tafi ne ya bar wa mutane.” [Muslim #2959]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Shikkhir (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na je na sami Manzon Allah (ﷺ) yana karanta wannan Surar, yana cewa: “Ɗan’adam yana cewa, \'Dukiyata, dukiyata\', shin kana da wani abu ne a dukiyarka in ban da wanda ka ci ka ƙarar, ko ka sanya a jikinka ka kashe, ko ka yi sadaka ka zartar?” [Ahmad #16305 da Muslim #2958]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Farkon ni’imar da za a tambayi bawa a kanta ranar alƙiyama shi ne za a ce masa: “Yanzu ashe ba mu ba ka lafiyar jiki ba? Muka kuma ƙosar da kai da ruwan sanyi?” [Tirmizi #3652 da Ibnu Hibban #7364 da Al-Hakim #7203]. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Wata rana Manzon Allah (ﷺ) ya fita sai ya haɗu da Abubakar da Umar a hanya, sai ya tambaye su ya ce: “Me ya fito da ku a wannan lokaci daga gidajenku?” Sai suka ce: “Yunwa, ya Manzon Allah.” Sai ya ce: “Na rantse da Allah, abin da ya fito da ku ni ma shi ne ya fito da ni, don haka ku taso.” Sai suka tashi, sai suka zo gidan wani mutumin Madina amma sai suka samu ba ya nan. Lokacin da matarsa ta ga Manzon Allah (ﷺ) sai ta ce: “Maraba lale-lale.” Sai Manzon Allah (ﷺ) ya tambaye ta, ina mai gidanta ya tafi? Sai ta amsa da cewa: “Ya tafi ya nemo mana ruwan sha.” Suna tsaye sai ga wannan mutum ya dawo, yana ganin Manzon Allah (ﷺ) da sahabbansa su biyu sai ya ce: “Na gode wa Allah, a yau babu wanda ya kai ni manyan baƙi.” Sai nan take ya fita ya je ya samu hantsar dabino burarre da nunanne, sai ya ce: “Ku ci wannan.” Sai ya ɗauki wuƙa, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa: “Kada ka kuskura ka yanka dabbar tatsa.” Sai ya yi musu yanka suka ci naman wannan akuya suka ci dabino, suka sha nono. Bayan sun ci sun ƙoshi, sun sha ruwa sun yi nak, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce wa Abubakar da Umar: “Na rantse da wanda raina yake a hannunsa, tabbas sai an yi muku tambaya game da wannan ni’imar a ranar alƙiyama.” [Muslim #2038].