العصر

Al-Asr

The Declining Day, Epoch · Surah 103 · Ayahs: 3 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. وَٱلۡعَصۡرِ

    Open ayah 103:1

    Na rantse da zamani.

  2. إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَفِي خُسۡرٍ

    Open ayah 103:2

    Lalle mutum yana cikin asara.

  3. إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلۡحَقِّ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلصَّبۡرِ

    Open ayah 103:3

    Sai dai waɗanda suka yi imani suka kuma yi ayyuka nagari, suka kuma yi wa juna wasiyya da gaskiya, suka kuma yi wa juna wasiyya da haƙuri. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da rantsuwa da zamani wanda ya ƙunshi dare da rana waɗanda su ne mahallin dukkan ayyukan bayi. Ya yi wannan rantsuwa ne kuwa domin ya tabbatar da cewa, duk wani ɗan’adam yana cikin asara a rayuwa, kowa da gwargwadon tasa asarar. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya togace wasu bayinsa daga aukawa cikin wannan asara, su ne kuwa waɗanda suka siffantu da siffofi huɗu: <b>Siffa ta farko, </b> imani da Allah da duk abin da ya umarci bawa ya yi imani da shi, wanda hakan ba zai yiwu ba sai da ilimin sanin Allah. <b>Siffa ta biyu, </b> aiki na ƙwarai, wannan kuwa ya ƙunshi duk ayyukan alheri na sarari da na ɓoye; masu alaƙa da haƙƙoƙin Allah, da masu alaƙa da haƙƙoƙin bayinsa, na wajibai ko na mustahabbai. <b>Siffa ta uku, </b> yi wa juna wasiyya da gaskiya, wadda ita ce kwaɗaitar da juna a kan yin imani da yin aiki nagari. <b>Siffa ta huɗu, </b> yi wa juna wasiyya a kan haƙuri wajen bin Allah da barin saɓa masa, da haƙuri da ƙaddararsa marar daɗi.