الهمزة
Al-Humaza
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَيۡلٞ لِّكُلِّ هُمَزَةٖ لُّمَزَةٍ
Open ayah 104:1Tsananin azaba ya tabbata ga duk wani mai yawan ƙyafice mai yawan suka.
ٱلَّذِي جَمَعَ مَالٗا وَعَدَّدَهُۥ
Open ayah 104:2Wanda ya tara dukiya ya ƙididdige ta.
يَحۡسَبُ أَنَّ مَالَهُۥٓ أَخۡلَدَهُۥ
Open ayah 104:3Yana zaton cewa dukiyarsa za ta dawwamar da shi.
كَلَّاۖ لَيُنۢبَذَنَّ فِي ٱلۡحُطَمَةِ
Open ayah 104:4Faufau! Tabbas lalle sai an jefa shi cikin (wutar) \'Huɗama\'.
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡحُطَمَةُ
Open ayah 104:5Me kuma ya sanar da kai irin girman \'Huɗama\'?
نَارُ ٱللَّهِ ٱلۡمُوقَدَةُ
Open ayah 104:6Wuta ce ta Allah abar hurawa.
ٱلَّتِي تَطَّلِعُ عَلَى ٱلۡأَفۡـِٔدَةِ
Open ayah 104:7Wadda take mamaye zukata.
إِنَّهَا عَلَيۡهِم مُّؤۡصَدَةٞ
Open ayah 104:8Lalle ita abar kullewa ce da su.
فِي عَمَدٖ مُّمَدَّدَةِۭ
Open ayah 104:9A cikin ginshiƙai miƙaƙƙu (da suka kewaye ta). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da gargaɗi mai tsanani ga mai yawan ƙyafice ga mutane, yana yawan sukan su da aibata su a bayan idanuwansu, inda Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi masa alƙawarin narko na azaba mai tsanani. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mai irin wannan mummunan hali da cewa, shi ne wanda babu abin da ya sa gaba a rayuwarsa sai tara dukiya da ƙididdige ta, don yana zaton dukiyar da ya tara ce za ta kuɓutar da shi daga mutuwa, sai ya yi ta rayuwa ta har abada a duniya. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsawatar masa da cewa, ba haka abin yake ba, lalle zai mutu ya koma ga Allah (Mai tsarki da daukaka), kuma lalle sai an jefa shi cikin wuta mai kakkarya duk wani abu da aka jefa cikinta, saboda matsanancin zafinta da azabarta. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wa Manzonsa (ﷺ) girman lamarin wannan wuta mai kakkarya komai, ya tambaye shi me ya sanar da shi ita ? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da amsa da cewa, ita wutarsa ce mai ruruwa, wadda azabarta take ratsa jikkunan kafirai zuwa zukatansu, ta ƙona kowace zuciya gwargwadon laifinta. Kuma ita wuta ce da za a kulle kafirai a cikinta ruf babu fita, za a yi ta gana musu azaba a cikin wasu dogayen ginshiƙai miƙaƙƙu da suka kewaye ta, don haka babu wata hanyar fita.