الفيل

Al-Fil

The Elephant · Surah 105 · Ayahs: 5 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. أَلَمۡ تَرَ كَيۡفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِأَصۡحَٰبِ ٱلۡفِيلِ

    Open ayah 105:1

    Shin ba ka ga yadda Ubangijinka Ya yi wa ma’abota giwa ba?

  2. أَلَمۡ يَجۡعَلۡ كَيۡدَهُمۡ فِي تَضۡلِيلٖ

    Open ayah 105:2

    Ashe bai mayar da makircinsu cikin watsewa ba?

  3. وَأَرۡسَلَ عَلَيۡهِمۡ طَيۡرًا أَبَابِيلَ

    Open ayah 105:3

    Ya kuma aiko musu da tsuntsaye dodo-dodo?

  4. تَرۡمِيهِم بِحِجَارَةٖ مِّن سِجِّيلٖ

    Open ayah 105:4

    Suna jifan su da duwatsu na ƙonanniyar laka?

  5. فَجَعَلَهُمۡ كَعَصۡفٖ مَّأۡكُولِۭ

    Open ayah 105:5

    Sai da Ya mayar da su kamar karmami da aka cinye? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da tunatar da Manzonsa (ﷺ) cewa, shin ba shi da masaniyar yadda ya yi wa ma’abota giwa, watau Abrahata da rundunarsa lokacin da suka nufi rushe Ɗakin Ka’aba? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar masa da cewa, ya mayar da mummunan makircinsu cikin watsewa, don kuwa ba su cim ma burinsu na raba mutane da Ɗakin Ka’aba da rusa shi baki ɗaya ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya aiko musu da tsuntsaye dodo-dodo, waɗanda suka riƙa jifan su da duwatsu na ƙonannen yumɓu, har sai da suka mayar da su kamar karmami da dabbobi suka ci suka tattake shi.