قريش

Quraish

Quraysh · Surah 106 · Ayahs: 4 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. لِإِيلَٰفِ قُرَيۡشٍ

    Open ayah 106:1

    Domin sabon da Ƙuraishawa suka yi.

  2. إِۦلَٰفِهِمۡ رِحۡلَةَ ٱلشِّتَآءِ وَٱلصَّيۡفِ

    Open ayah 106:2

    Sabonsu na yin safara a lokacin ɗari (zuwa ƙasar Yaman) da lokacin bazara (zuwan ƙasar Sham).

  3. فَلۡيَعۡبُدُواْ رَبَّ هَٰذَا ٱلۡبَيۡتِ

    Open ayah 106:3

    To sai su bauta wa Ubangijin wannan Ɗakin.

  4. ٱلَّذِيٓ أَطۡعَمَهُم مِّن جُوعٖ وَءَامَنَهُم مِّنۡ خَوۡفِۭ

    Open ayah 106:4

    Wanda Ya ciyar da su daga yunwa, Ya kuma amintar da su daga tsoro. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da tunatar da Ƙuraishawa abin da suka saba da shi na tafiye-tafiye don kasuwancinsu; zuwa Yaman a lokacin sanyi; da kuma zuwa Sham a lokacin zafi, cikin aminci ba tare da tsoron komai ba. Saboda haka sai ya umarce su da su bauta wa Ubangijin Ɗaki mai alfarma shi kaɗai, watau Ka’aba, domin kuwa shi ne ya hore musu waɗannan tafiye-tafiye, kuma ya ciyar da su, ya raba su da yunwa, ya kuma amintar da su, suna rayuwa babu wata fargaba ko tsoro. Wannan kuwa saboda ya sanya ganin girman Ɗakinsa da girmama mutanen Makka a cikin zukatan sauran Larabawa.