الماعون

Al-Maa'un

Almsgiving · Surah 107 · Ayahs: 7 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. أَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي يُكَذِّبُ بِٱلدِّينِ

    Open ayah 107:1

    Shin ka ga wanda yake ƙaryata ranar sakamako?

  2. فَذَٰلِكَ ٱلَّذِي يَدُعُّ ٱلۡيَتِيمَ

    Open ayah 107:2

    To shi ne wanda yake ingije maraya (daga haƙƙinsa).

  3. وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلۡمِسۡكِينِ

    Open ayah 107:3

    Ba kuma ya kwaɗaitarwa wajen ciyar da miskini.

  4. فَوَيۡلٞ لِّلۡمُصَلِّينَ

    Open ayah 107:4

    To tsananin azaba ya tabbata ga masallata.

  5. ٱلَّذِينَ هُمۡ عَن صَلَاتِهِمۡ سَاهُونَ

    Open ayah 107:5

    Waɗanda suke masu rafkana su bar sallarsu.

  6. ٱلَّذِينَ هُمۡ يُرَآءُونَ

    Open ayah 107:6

    Waɗanda su ne suke yin riya.

  7. وَيَمۡنَعُونَ ٱلۡمَاعُونَ

    Open ayah 107:7

    Suke kuma hana kayan taimako. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da zargin mutumin da yake tozarta haƙƙoƙinsa da na bayinsa, inda ya tambayi Manzonsa (ﷺ) cewa, ko ya san wanda yake ƙaryata ranar sakamako, watau alƙiyama? Sai kuma ya bayyana masa shi da cewa, shi ne wanda yake ture maraya da ƙarfi daga haƙƙinsa ko buƙatarsa, saboda ƙeƙashewar zuciyarsa da rashin imaninsa, kuma ba ya kwaɗaitar da kansa ko ya kwaɗaitar da wani a kan ciyar da mabuƙaci. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi alƙawarin azaba mai tsanani da hallaka ga masallatan da suke shagala ba sa yin sallolinsu a kan lokaci, ko ma su bar sallar a wasu lokuta ba tare da sun yi ta ba. Kuma dai su ne waɗanda suke yin sallolinsu da sauran ayyukansu na ibada don mutane su gani su yaba, watau don riya, ba sa tsantsanta ibadunsu ga Allah (Mai tsarki da daukaka) shi kaɗai. Su ne kuma waɗanda ba sa taimaka wa mutane da komai; ba sa ba su zakkar dukiyarsu, kuma ba sa taimaka musu idan sun buƙaci taimako, ko sun roƙi aron ababan amfani, kamar tukunya ko gatari ko guga da makamantansu.