الكوثر
Al-Kawthar
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
إِنَّآ أَعۡطَيۡنَٰكَ ٱلۡكَوۡثَرَ
Open ayah 108:1Lalle Mu Mun ba ka alheri mai yawa.
فَصَلِّ لِرَبِّكَ وَٱنۡحَرۡ
Open ayah 108:2To sai ka yi salla don Ubangijinka, ka kuma soke (abin hadayarka).
إِنَّ شَانِئَكَ هُوَ ٱلۡأَبۡتَرُ
Open ayah 108:3Lalle mai ƙin ka shi ne mai yankakken alheri. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa, ya ba shi alheri mai yawa, watau ƙoramar Alkausara ta gidan Aljanna. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ɗan yi gyangyaɗi sai ya ɗago kansa yana murmushi, ya ce: “Ɗazu an saukar mini wata sura.” Sai ya karanta Bisimilla har zuwa ƙashen wannan Surar. Sannan ya ce: “Shin kun san mene ne ‘Al-Kausar’?” Sai suka ce: “Allah da Manzonsa su suka fi sani.” Sai ya ce: “Ƙorama ce da Ubangijina ya ba ni a Aljanna, tana tattare da alheri mai yawa, al’ummata kuma a ranar alƙiyama za su sha ruwanta. Ƙoranta adadin taurari ne. Za a janye wani bawa daga cikinsu, sai in ce: “Ya Ubangijina, yana daga cikin al’ummata”, sai a ce mini: ‘Lalle kai ba ka san abin da ya farar a bayanka ba.’” [Muslim #400]. An karɓo daga Anas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Na shiga Aljanna, sai na ga wata ƙorama gefe da gefenta hemomi ne na lu’ulu’u, sai na sanya hannuna inda ruwa yake gudana a cikinta, sai na ji wani ƙanshin turaren almiski mai daɗi, sai na ce: ‘Ya Jibrilu, mene ne wannan kuma?’ Sai ya ce: “Wannan shi ne ‘Alkausar ’ wanda Allah ya ba ka.’” [Bukhari #658]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya yi masa godiya a kan wannan babbar ni’imar da ya yi masa ta hanyar yin salla da yanka dominsa shi kaɗai ba tare da wani abokin tarayya ba, saɓanin abin da mushirikai suke yi na kusantar ababan bautarsu, ta yi musu yanka da bauta musu. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa Manzonsa (ﷺ) cewa, maƙiyinsa shi ne mai yankakken alheri, wanda a duk sanda aka tuna shi za a yi tir da shi.