الكافرون

Al-Kaafiroon

The Disbelievers · Surah 109 · Ayahs: 6 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. قُلۡ يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡكَٰفِرُونَ

    Open ayah 109:1

    Ka ce: “Ya ku waɗannan kafirai.

  2. لَآ أَعۡبُدُ مَا تَعۡبُدُونَ

    Open ayah 109:2

    “Ba zan bauta wa abin da kuke bauta wa ba.

  3. وَلَآ أَنتُمۡ عَٰبِدُونَ مَآ أَعۡبُدُ

    Open ayah 109:3

    “Ku kuma ba masu bautar abin da nake bauta wa ba ne.

  4. وَلَآ أَنَا۠ عَابِدٞ مَّا عَبَدتُّمۡ

    Open ayah 109:4

    “Ni kuma ba mai bauta wa abin da kuka bauta wa ba ne.

  5. وَلَآ أَنتُمۡ عَٰبِدُونَ مَآ أَعۡبُدُ

    Open ayah 109:5

    “Ku ma ba za ku bauta wa abin da nake bauta wa ba.

  6. لَكُمۡ دِينُكُمۡ وَلِيَ دِينِ

    Open ayah 109:6

    “Addininku na gare ku, ni ma kuma addinina na gare ni.” Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da umartar Manzonsa (ﷺ) da cewa, ya fito sarari ya faɗa wa kafirai cewa, shi fa ko nan gaba ba zai bauta wa gumakan da suke bauta wa ba, su ma kuma a halin yanzu ba sa bauta wa abin da shi yake bauta wa, domin shi yana bautar Allah ne shi kaɗai, su kuma suna haɗa shi da wasu ababan bauta. Ya kuma ƙara tabbatar musu da cewa, shi a halin da ake ciki ba mai bautar abin da suke bauta wa ba ne, hakanan su ma ko nan gaba, ba masu bautar abin da yake bauta wa ne ba. Saboda haka ya shaida musu cewa, suna da addininsu na kafirci da suke bi, shi ma yana da nasa addini na Musulunci da yake kai, watau dai hanyar jirgi daban ta mota ma daban, ba za su taɓa haɗuwa ba.