النصر

An-Nasr

Divine Support · Surah 110 · Ayahs: 3 · Medinan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. إِذَا جَآءَ نَصۡرُ ٱللَّهِ وَٱلۡفَتۡحُ

    Open ayah 110:1

    Idan nasarar Allah ta zo da kuma buɗe (Makka).

  2. وَرَأَيۡتَ ٱلنَّاسَ يَدۡخُلُونَ فِي دِينِ ٱللَّهِ أَفۡوَاجٗا

    Open ayah 110:2

    Ka kuma ga mutane suna shiga addinin Allah ƙungiya-ƙungiya.

  3. فَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ وَٱسۡتَغۡفِرۡهُۚ إِنَّهُۥ كَانَ تَوَّابَۢا

    Open ayah 110:3

    To ka yi tasbihi da yabon Ubangijinka, ka kuma nemi gafararsa. Lalle Shi Ya kasance Mai karɓar tuba ne. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da yi wa Manzonsa (ﷺ) albishir da samun gagarumar nasara da buɗe garin Makka, sannan zai ga mutane ƙungiya-ƙungiya suna ta shiga addinin Musulunci bayan a da suna gaba da shi. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Lokacin da wannan Surar ta sauka, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Mutanen Yaman sun zo, masu sanyin hali. Imani Bayamane ne, fahimta ma Bayamaniya ce, hikima ma Bayamaniya ce.” [Ahmad #7723]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarce shi da cewa, yayin da ya ga waɗannan abubuwa sun auku, to ya sani wannan alama ce mai nuna aikinsa na manzanci ya zo ƙarshe, sai ya duƙufa wajen yi wa Ubangijinsa tasbihi tare da gode masa bisa ga ni’imar nasara da cin garin Makka da yaƙi da ya ba shi, ya kuma nemi gafararsa, domin shi Allah mai yawan karɓar tuban bayinsa ne mai gafarta musu. An karɓo daga A’isha (Allah ya kara mata yarda) ta ce: Manzon Allah (ﷺ) ya kasance yana yawan faɗar: Subhanallahi wa bi hamdihi wa astagfirullaha wa atubu ilaih , sai na ce: Ya Manzon Allah, na ga kana ta yawaita faɗar waɗannan kalmomi. Sai ya ce: “Ubangijina ne ya bayyana min cewa, zan ga wata alama a cikin al’ummata, idan na gan ta, to in yawaita faɗar waɗannan kalmomin, to haƙiƙa na gan ta ita ce (sai ya karanta wannan Surar, ya fassara ‘buɗi’ da buɗe Makka).” [Muslim #484]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Umar (Allah ya kara masa yarda) ya tambayi sahabbai abin da suka fahimta daga wannan Surar sai suka ce, ana nufin buɗe garin \'Mada’in\' da cinye manyan fada-fada na Farisawa. Sai ya tambaye ni, ni kuma sai na ce: Misali ne aka ba Muhammad (ﷺ), aka sanar da shi lokacin mutuwarsa ya yi.” [Bukhari #4969].