المسد

Al-Masad

The Palm Fibre · Surah 111 · Ayahs: 5 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. تَبَّتۡ يَدَآ أَبِي لَهَبٖ وَتَبَّ

    Open ayah 111:1

    Hannayen Abu Lahabi sun halaka, shi ma kuma ya halaka.

  2. مَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُ مَالُهُۥ وَمَا كَسَبَ

    Open ayah 111:2

    Dukiyarsa da abin da ya tsuwurwurta ba su amfana masa komai ba.

  3. سَيَصۡلَىٰ نَارٗا ذَاتَ لَهَبٖ

    Open ayah 111:3

    Ba da daɗewa ba zai shiga wuta mai balbali.

  4. وَٱمۡرَأَتُهُۥ حَمَّالَةَ ٱلۡحَطَبِ

    Open ayah 111:4

    Da kuma matarsa mai yawan ɗaukar kayan ƙaya.

  5. فِي جِيدِهَا حَبۡلٞ مِّن مَّسَدِۭ

    Open ayah 111:5

    A wuyanta akwai igiyar kaba mai ingantacciyar tukka. (a ranar alƙiyama). Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da bayanin wannan mummunan narko da ya yi wa Abu Lahab wanda ya gaya wa Manzon Allah (ﷺ) baƙar magana don ya gargaɗe su game da azabar Allah idan ba su yi imani ba. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, hannayen Abu Lahab sun hallaka, shi ma kansa ya hallaka, domin ya yi asarar ayyukansa, tun da har ya zamanto mai cutar da Manzon Allah (ﷺ). Ban da wannan kuma, dukiyarsa da ya tara yake kuma tinƙaho da ita, za ta tafi a banza ba za ta amfana masa komai ba, hakanan ‘ya’yansa da yake ji da su, ba za su yi masa amfanin komai ba, domin duk ba za su kare shi daga azabar Allah ba a ranar alƙiyama. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi masa alƙawarin cewa ba da jimawa ba zai ƙona shi da wutarsa mai balbali mai tsananin zafi; dukiyarsa da ‘ya’yansa ba za su jawo masa wani jin daɗi ba ko rahama. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, ita ma matarsa wadda ake kira Ummu Jamil za ta shiga wuta tare da mijinta Abu Lahab, domin ita ma tana cutar da Manzon Allah (ﷺ) yayin da take zuba masa ƙaya a kan hanyarsa, domin idan ya zo wucewa ya taka. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, za a sa mata igiyar kaba mai ingantacciyar tukka a kyakkyawan wuyan nan nata da take taƙama da shi, a ja ta da ita zuwa wutar Jahannama.