الإخلاص
Al-Ikhlaas
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
قُلۡ هُوَ ٱللَّهُ أَحَدٌ
Open ayah 112:1Ka ce: “Shi ne Allah Ɗaya.
ٱللَّهُ ٱلصَّمَدُ
Open ayah 112:2“Allah Abin nufa da buƙatu.
لَمۡ يَلِدۡ وَلَمۡ يُولَدۡ
Open ayah 112:3“Bai haifa ba, kuma ba a haife Shi ba.
وَلَمۡ يَكُن لَّهُۥ كُفُوًا أَحَدُۢ
Open ayah 112:4“Kuma babu wani da ya kasance kini a gare Shi.” Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya furta cewa, lalle Allah (Mai tsarki da daukaka) Ɗaya ne, ya kaɗaita da cancantar a bauta masa, babu wani abin bauta sai shi kaɗai. Shi ne kuma abin nufa da buƙata, wanda shugabanci ya tuƙe zuwa gare shi, domin ya tattara duk siffofin kalama da ɗaukaka. Yana daga cikin kamalarsa cewa, shi bai haifi komai ba, ba kuma wanda ya haife shi, don haka ba shi da ɗa ba shi da mahaifi. Sannan kuma babu wani ɗaya cikin halittunsa da ya zamanto kini a gare shi, domin babu mai kama da shi a sunayensa da siffofinsa da ayyukansa.