الفلق

Al-Falaq

The Dawn · Surah 113 · Ayahs: 5 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلۡفَلَقِ

    Open ayah 113:1

    Ka ce: “Ina neman tsari da Ubangijin asuba.

  2. مِن شَرِّ مَا خَلَقَ

    Open ayah 113:2

    “Daga sharrin abin da Ya halitta.

  3. وَمِن شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ

    Open ayah 113:3

    “Da kuma sharrin dare idan ya lulluɓe da duhu.

  4. وَمِن شَرِّ ٱلنَّفَّٰثَٰتِ فِي ٱلۡعُقَدِ

    Open ayah 113:4

    “Da kuma sharrin mata masu tofi a cikin ƙulle-ƙulle.

  5. وَمِن شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ

    Open ayah 113:5

    “Da kuma sharrin mai hassada yayin da ya yi hassadar.” Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da umartar Manzonsa (ﷺ) da ya nemi tsari da kariyar Ubangijin asuba daga sharrin duk wani mahaluƙi mai cutarwa, mutum ne ko aljani ko dabba. Ya kuma nemi tsarinsa daga sharrin duk wani abu da sharrinsa yake bayyana a cikin dare yayin da ya lulluɓe da duhunsa, kamar wasu miyagun dabbobi ko ƙwari ko ɓarayi. Ya kuma nemi tsari daga sharrin mata masu sihiri waɗanda suke tofi a cikin ƙulle-ƙullensu na sihiri. Ya kuma nemi tsarinsa daga duk wani mahassadi idan ya yi aiki da abin da hassadarsa ke saƙa masa.