الناس
An-Naas
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلنَّاسِ
Open ayah 114:1Ka ce: “Ina neman tsari da Ubangijin mutane.
مَلِكِ ٱلنَّاسِ
Open ayah 114:2“Sarkin mutane.
إِلَٰهِ ٱلنَّاسِ
Open ayah 114:3“Abin bautar mutane.
مِن شَرِّ ٱلۡوَسۡوَاسِ ٱلۡخَنَّاسِ
Open ayah 114:4“Daga sharrin mai sa wasuwasi, mai noƙewa.
ٱلَّذِي يُوَسۡوِسُ فِي صُدُورِ ٱلنَّاسِ
Open ayah 114:5“Wanda yake yin wasuwasi a cikin ƙirazan mutane.
مِنَ ٱلۡجِنَّةِ وَٱلنَّاسِ
Open ayah 114:6“Daga aljannu da na mutane.” Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe Surar da umartar Manzonsa (ﷺ) da ya nemi tsarin Ubangijin mutane, kuma Sarkinsu mai cikakken iko da yin yadda ya ga dama da su, abin bautarsu na gaskiya wanda babu wani abin bauta da gaskiya sai shi kaɗai. Ya yi masa tsari daga sharrin Shaiɗan wanda yake jefa waswasinsa ga ɗan’adam idan ya gafala ya manta da ambaton Allah, mai noƙewa ya ja baya duk sanda ɗan’adam ya ambaci Allah. Yana jefa waswasinsa cikin zukatan mutane. Kuma wannan shaiɗani ana samun sa cikin mutane kamar yadda ake samun sa a cikin aljannu.