الملك

Al-Mulk

The Sovereignty · Surah 67 · Ayahs: 30 · Meccan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. تَبَٰرَكَ ٱلَّذِي بِيَدِهِ ٱلۡمُلۡكُ وَهُوَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٌ

    Open ayah 67:1

    Wanda mulki yake a hannunsa alhairansa sun yawaita, kuma Shi Mai iko ne a kan komai.

  2. ٱلَّذِي خَلَقَ ٱلۡمَوۡتَ وَٱلۡحَيَوٰةَ لِيَبۡلُوَكُمۡ أَيُّكُمۡ أَحۡسَنُ عَمَلٗاۚ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡغَفُورُ

    Open ayah 67:2

    Wanda Ya halicci mutuwa da rayuwa don Ya jarraba ku (Ya bayyana) wane ne a cikinku ya fi kyakkyawan aiki? Shi kuma Mabuwayi ne, Mai gafara.

  3. ٱلَّذِي خَلَقَ سَبۡعَ سَمَٰوَٰتٖ طِبَاقٗاۖ مَّا تَرَىٰ فِي خَلۡقِ ٱلرَّحۡمَٰنِ مِن تَفَٰوُتٖۖ فَٱرۡجِعِ ٱلۡبَصَرَ هَلۡ تَرَىٰ مِن فُطُورٖ

    Open ayah 67:3

    Wanda Ya halicci sammai bakwai hawa-hawa; ba za ka ga wata tangarɗa cikin halittar (Allah) Mai rahama ba. Ka maimaita dubanka, shin za ka ga wata tsaga?

  4. ثُمَّ ٱرۡجِعِ ٱلۡبَصَرَ كَرَّتَيۡنِ يَنقَلِبۡ إِلَيۡكَ ٱلۡبَصَرُ خَاسِئٗا وَهُوَ حَسِيرٞ

    Open ayah 67:4

    Sannan ka sake mayar da gani sau da yawa, ganin zai dawo maka a ƙasƙance, shi kuma yana a dakushe (bai ga wata tsaga ba).

  5. وَلَقَدۡ زَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنۡيَا بِمَصَٰبِيحَ وَجَعَلۡنَٰهَا رُجُومٗا لِّلشَّيَٰطِينِۖ وَأَعۡتَدۡنَا لَهُمۡ عَذَابَ ٱلسَّعِيرِ

    Open ayah 67:5

    Kuma haƙiƙa Mun ƙawata saman duniya da taurari Muka sanya su kuma ababan jifan shaiɗanu; Muka kuma tanadar musu azabar (wutar) Sa’ira. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Sura da yi wa kansa kirari da cewa shi ne wanda mulkin komai yake a hannunsa albarkatunsa da alheransa kuma sun yawaita sun mamaye ko’ina da ina a sama da ƙasa, kuma shi mai iko ne a kan komai, babu wani abu da yake gagarar sa ko yake fita daga ƙarƙashin ikonsa. Sannan ya bayyana wasu dalilai na Ƙudurarsa da cewa, shi ne wanda ya halicci mutuwa da rayuwa, ya ƙaddara za su faru ga bayinsa, don ya jarrabe su ya bayyana wane ne a cikinsu ya fi kyakkyawan aiki. Kuma shi Mabuwayi ne wanda babu mai rinjayar sa, kuma mai gafara ne ga bayinsa masu laifi idan su tuba. Hakanan daga cikin dalilan Ƙudurarsa da ikonsa, shi ne wanda ya halicci sammai bakwai hawa-hawa, watau wata a saman wata da tazara tsakanin kowace sama da ‘yar’uwarta, ya kuma inganta halittarsu ta yadda mutum ba zai iya ganin wata tangarɗa ko zoɓawa ba a tare da su, duk kuwa yadda mutum ya kai ga naci da ƙura ido ba zai taɓa ganin wata ɓaraka ba a jikinsu. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya sake umartar mutum ya sake ƙura idanunsa sosai ko zai ga wata tawaya a halittar sammai, Allah ya tabbatar da cewa, hakanan zai yi har ya gaji ba tare da ya ga wani abin kushewa ba. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana tsananin kyau da ƙaye da sama take da shi, domin ya ƙawata ta da taurari masu haske kamar fitilu da daddare, sannan ya mayar da su harshen wuta na jifan shaiɗanu masu ƙoƙarin satar ji su ƙona su, a lahira kuwa ya tanadar musu azabar wutar Jahannama, saboda kafircin da suke yi da kuma jefa bayinsa cikin ɓata.

  6. وَلِلَّذِينَ كَفَرُواْ بِرَبِّهِمۡ عَذَابُ جَهَنَّمَۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

    Open ayah 67:6

    Waɗanda kuma suka kafirce wa Ubangijinsu suna da azabar Jahannama; makoma kuwa ta munana.

  7. إِذَآ أُلۡقُواْ فِيهَا سَمِعُواْ لَهَا شَهِيقٗا وَهِيَ تَفُورُ

    Open ayah 67:7

    Idan aka jefa su a cikinta sai su ji kururuwarta, tana tafarfasa.

  8. تَكَادُ تَمَيَّزُ مِنَ ٱلۡغَيۡظِۖ كُلَّمَآ أُلۡقِيَ فِيهَا فَوۡجٞ سَأَلَهُمۡ خَزَنَتُهَآ أَلَمۡ يَأۡتِكُمۡ نَذِيرٞ

    Open ayah 67:8

    Tana kusa da ta kekkece saboda tsananin fushi; duk sanda aka jefa wata tawaga a cikinta sai masu tsaron ta su tambaye su: “Shin mai gargaɗi bai zo muku ba?”

  9. قَالُواْ بَلَىٰ قَدۡ جَآءَنَا نَذِيرٞ فَكَذَّبۡنَا وَقُلۡنَا مَا نَزَّلَ ٱللَّهُ مِن شَيۡءٍ إِنۡ أَنتُمۡ إِلَّا فِي ضَلَٰلٖ كَبِيرٖ

    Open ayah 67:9

    Sai su ce, “E, haka ne, haƙiƙa mai gargaɗi ya zo mana, sai muka ƙaryata, muka kuma ce, Allah bai saukar da wani abu ba, ba kwa a kan komai sai ɓata mai girma.”

  10. وَقَالُواْ لَوۡ كُنَّا نَسۡمَعُ أَوۡ نَعۡقِلُ مَا كُنَّا فِيٓ أَصۡحَٰبِ ٱلسَّعِيرِ 

    Open ayah 67:10

    Suka kuma ce: “Da mun kasance muna fahimta ko kuma muna hankalta, to da ba mu kasance cikin ‘yan (wutar) Sa’ira ba.”

  11. فَٱعۡتَرَفُواْ بِذَنۢبِهِمۡ فَسُحۡقٗا لِّأَصۡحَٰبِ ٱلسَّعِيرِ

    Open ayah 67:11

    Sai suka amsa laifinsu, sai (a ce da su): “Can dai da ‘yan (wutar) Sa’ira.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana mummunan halin da kafirai za su tsinci kansu a cikinsa a ranar alƙiyama, inda ya tabbatar musu cewa, wutar Jahannama mai ruruwa tana jiran su ranar alƙiyama, ita ce makomarsu ta ƙarshe, wannan makoma tasu kuwa ta munana matuƙa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, yayin da za a jefa su cikin wutar Jahannama za su ji tana hargagi da sauti mai ɗaga hankali tana tafarfasa, kamar za ta tsage don tsananin hushi da duk wani wanda za a jefa shi cikinta. Kuma duk sanda aka jefa wata ƙungiya ta kafirai a cikinta sai mala’iku masu tsaron ta su tambaye su cikin zargi da tuhuma cewa, shin ba wani mai gargaɗi da ya zo musu yana tsoratar da su azabar Allah? Sai kafirai su amsa musu da cewa, e, lalle manzo mai gargaɗi ya zo musu ya kuma tsoratar da su azabar Allah, to amma sai taurin kansu ya sanya suka ƙaryata shi har ma suka faɗa masa cewa, babu wani wahayi da aka yi masa, suka zargi manzannin Allah da cewa, ba a kan komai suke ba sai ɓata mai girma. Sannan sai kafirai ‘yan wuta suka ci gaba da zargin kansu da nadama a lokacin da nadama ba za ta amfana musu komai ba, suna faɗar cewa, da a ce sun kasance masu sauraro irin na basira ko sun yi aiki da hankalinsu, sun tsaya sun nutsu sun bambance tsakanin ƙarya da gaskiya, da ba su tsinci kansu cikin ‘yan wuta ba, domin da sun yi imani da manzannin Allah sun gaskata abin da suka zo da shi na gaskiya, to da sun zama ‘yan Aljanna. Don haka sai suka yi iƙirari da laifinsu da bakinsu, suka tabbatar cewa sun yi kafirci sun ƙaryata manzannin Allah, don haka sun cancanci shiga wutar Jahannama. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi tir da ‘yan wuta ya nesanta su daga rahamarsa. An karɓo daga Abul Bakhtari Aɗ-Ɗa’i ya ce, wani wanda ya ji wannan hadisi daga Manzon Allah ya faɗa min cewa, Annabi (ﷺ) ya ce: “Ba za a hallakar da mutane ba har sai su da kansu sun yanke wa kansu hanzari.” [Ahmad #28342 da Abu Dawud #4347].

  12. إِنَّ ٱلَّذِينَ يَخۡشَوۡنَ رَبَّهُم بِٱلۡغَيۡبِ لَهُم مَّغۡفِرَةٞ وَأَجۡرٞ كَبِيرٞ

    Open ayah 67:12

    Lalle waɗanda suke tsoron Ubangijinsu ba tare da suna ganin sa ba, suna da gafara da kuma lada mai girma.

  13. وَأَسِرُّواْ قَوۡلَكُمۡ أَوِ ٱجۡهَرُواْ بِهِۦٓۖ إِنَّهُۥ عَلِيمُۢ بِذَاتِ ٱلصُّدُورِ

    Open ayah 67:13

    Da ku ɓoye zancenku ko ku bayyana shi, lalle Shi Masanin abin da yake cikin zukata ne.

  14. أَلَا يَعۡلَمُ مَنۡ خَلَقَ وَهُوَ ٱللَّطِيفُ ٱلۡخَبِيرُ

    Open ayah 67:14

    Yanzu wanda ya yi halitta ba zai san ta ba? Shi ne kuma Mai tausasawa Masani.

  15. هُوَ ٱلَّذِي جَعَلَ لَكُمُ ٱلۡأَرۡضَ ذَلُولٗا فَٱمۡشُواْ فِي مَنَاكِبِهَا وَكُلُواْ مِن رِّزۡقِهِۦۖ وَإِلَيۡهِ ٱلنُّشُورُ

    Open ayah 67:15

    Shi ne wanda Ya sanya muku ƙasa horarriya, saboda haka ku yi tafiya a cikin sasanninta kuma ku ci daga arzikinta; makoma kuwa zuwa gare Shi take. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa muminai masu tsoron sa a lokacin da suka kaɗaita da kawunansu cewa, suna da gafarar zunubansu, kuma suna da wani lada mai girma, ita ce Aljanna. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa mutane cewa, da su ɓoye zancensu ko su bayyana shi a fili duk daidai suke a wurinsa, domin shi masanin abin da yake cikin zukatan bayinsa ne, babu abin da zai ɓuya a gare shi. Domin kuwa ba zai yiwu a ce wanda ya ƙagi halitta ya kasa sanin sirrin waɗannan halittu nasa ba, alhalin shi mai tausasa wa bayinsa ne, masanin dukkan al’amuransu ne, babu abin da yake ɓuya a gare shi. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wa bayinsa wata babbar ni’ima da ya yi musu ta hore musu bayan ƙasa har ta zamanto mai sauƙin zama da rayuwa a kanta, ba tare da tana tangal-tangal da su ba, don haka ya umarce su da su yi tafiye-tafiyensu a cikin sassanta da ɓangarorinta domin neman arziki da ya sanya a ko’ina a cikinta, kuma su ci daga wannan arzikin nasa wanda ya tanade shi saboda su, su kuma yi wa kansu kyakkyawan shiri na haɗuwa da shi, don kuwa makomarsu gaba ɗaya zuwa gare shi ne, domin yi musu hisabi da sakamako.

  16. ءَأَمِنتُم مَّن فِي ٱلسَّمَآءِ أَن يَخۡسِفَ بِكُمُ ٱلۡأَرۡضَ فَإِذَا هِيَ تَمُورُ

    Open ayah 67:16

    Yanzu kun amince cewa wanda Yake sama Ya kifar da ƙasa da ku, sai kawai ku gan ta tana ta tambal-tambal?

  17. أَمۡ أَمِنتُم مَّن فِي ٱلسَّمَآءِ أَن يُرۡسِلَ عَلَيۡكُمۡ حَاصِبٗاۖ فَسَتَعۡلَمُونَ كَيۡفَ نَذِيرِ

    Open ayah 67:17

    Ko kuma kun amince cewa wanda Yake sama Ya aiko muku da guguwa mai tsakwankwani? To da sannu za ku san yadda (sakamakon) gargaɗina zai zama.

  18. وَلَقَدۡ كَذَّبَ ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِهِمۡ فَكَيۡفَ كَانَ نَكِيرِ

    Open ayah 67:18

    Haƙiƙa kuma waɗanda suke gabaninku sun ƙaryata, to yaya (sakamakon) nuna ƙin amincewata ya zama?

  19. أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَى ٱلطَّيۡرِ فَوۡقَهُمۡ صَٰٓفَّٰتٖ وَيَقۡبِضۡنَۚ مَا يُمۡسِكُهُنَّ إِلَّا ٱلرَّحۡمَٰنُۚ إِنَّهُۥ بِكُلِّ شَيۡءِۭ بَصِيرٌ

    Open ayah 67:19

    Shin ba sa ganin tsuntsaye a samansu suna shimfiɗa (fikafikansu) suna kuma rufe su? Ba wanda yake riƙe da su sai (Allah) Mai rahma. Lalle Shi Mai ganin komai ne. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankulan mutane zuwa ga lura da wasu ayoyi masu nuna girman Ƙudurarsa da cikar Mulkinsa, tare da tsoratar da su game da saɓa masa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tambaye su cewa, yanzu sun amince Allah (Mai tsarki da daukaka) wanda yake sama cewa ba zai kifar da ƙasa da su ta haɗiye su ba, kamar yadda ya yi wa Ƙaruna, sai kawai su gan ta tana tambal-tambal da su bayan a da suna zaune lafiya a kanta? Ko kuma sun amince da cewa wanda yake sama, watau Allah ba zai aiko musu da duwatsu daga sama ba, kamar yadda ya yi wa mutanen Annabi Luɗu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) ruwan duwatsu daga sama ya hallaka su? Allah (Mai tsarki da daukaka) ya razana su da cewa ba da jimawa ba za su san yadda sakamakon gargaɗinsa zai zama, watau lokacin da za su ga azaba ta nufo su gadan-gadan, a lokacin babu wata nadama da za ta yi musu amfani. An karɓo daga Mu’awiya ɗan Hakim (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Na mari wata baiwata bayan ta yi sakaci har kyarkeci ya cinye min akuyata, sai kuma na yi nadama, na zo da ita wajen Manzon Allah (ﷺ) na ce: Ya Manzon Allah, shin ba na ‘yanta ta ba? Sai Manzon Allah (ﷺ) ya tambaye ta: “Ina Allah yake?” Sai ta ce: “Yana sama.” Sai ya ce mata: “Ni wane ne?” Sai ta ce: “Kai Manzon Allah ne.” Sai ya ce: “Ka ‘yanta ta, domin ita mumina ce.” [Muslim #537 da Abu Dawud #930]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Masu tausayawa, Allah mai rahama yana tausaya musu, ku tausaya wa wanda yake ƙasa sai wanda yake sama ya tausaya muku.” [Abu Dawud #4941 da Tirmizi #1924 da Ahmad #6494]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar wa mushirikai cewa, al’ummun da suka gabace su sun ƙaryata manzannin Allah, sai azabar Allah ta sauko musu yayin da suka doge a kan kafirci da tsaurin kai, to su duba su ga yadda sakamakon inkarinsa a gare su ya zama, domin ya zama sakamako ne mai tsanani, don haka su ma mushirikai su yi hattara kada su jawo wa kawunansu irin wannan mummunan sakamako a duniya da lahira. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana wata babbar aya da ke nuna cikar Ƙudurarsa da ikonsa, yayin da ya tambayi mutane cewa, shin ba su ga yadda tsuntsaye suke tashi cikin sararin sama ba, suna tafiya sahu-sahu cikin natsuwa da walwala, babu mai riƙe su ya hana su faɗowa ƙasa sai Allah Mai rahama? Lalle shi Allah mai ganin komai ne, babu abin da yake ɓuya a gare shi.

  20. أَمَّنۡ هَٰذَا ٱلَّذِي هُوَ جُندٞ لَّكُمۡ يَنصُرُكُم مِّن دُونِ ٱلرَّحۡمَٰنِۚ إِنِ ٱلۡكَٰفِرُونَ إِلَّا فِي غُرُورٍ 

    Open ayah 67:20

    Ko kuwa wace runduna ce kuke da ita da za ta taimaka muku ba (Allah) Mai rahama ba? Su dai kafirai ba sa kan komai sai ruɗi.

  21. أَمَّنۡ هَٰذَا ٱلَّذِي يَرۡزُقُكُمۡ إِنۡ أَمۡسَكَ رِزۡقَهُۥۚ بَل لَّجُّواْ فِي عُتُوّٖ وَنُفُورٍ

    Open ayah 67:21

    Ko kuwa wane ne zai arzuta ku idan (Allah) Ya riƙe arzikinsa? A’a, kawai dai sun yi zurfi ne cikin taurin kai da fanɗarewa.

  22. أَفَمَن يَمۡشِي مُكِبًّا عَلَىٰ وَجۡهِهِۦٓ أَهۡدَىٰٓ أَمَّن يَمۡشِي سَوِيًّا عَلَىٰ صِرَٰطٖ مُّسۡتَقِيمٖ

    Open ayah 67:22

    Shin wanda yake tafiya a kife a kan fuskarsa shi ya fi zama a kan daidai ko kuma wanda yake tafiya a miƙe kan hanya madaidaiciya?

  23. قُلۡ هُوَ ٱلَّذِيٓ أَنشَأَكُمۡ وَجَعَلَ لَكُمُ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡأَبۡصَٰرَ وَٱلۡأَفۡـِٔدَةَۚ قَلِيلٗا مَّا تَشۡكُرُونَ

    Open ayah 67:23

    Ka ce: “Shi ne (Allah) Wanda Ya fare ku Ya kuma sanya muku ji da gani da zukata; kaɗan ne kawai kuke godewa.”

  24. قُلۡ هُوَ ٱلَّذِي ذَرَأَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَإِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ

    Open ayah 67:24

    Ka ce: “Shi ne wanda Ya halicce ku a kan ƙasa, kuma zuwa gare Shi za a tattara ku.”

  25. وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا ٱلۡوَعۡدُ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ

    Open ayah 67:25

    Suna kuma cewa: “Yaushe ne wannan alƙawarin, idan kun kasance masu gaskiya?”

  26. قُلۡ إِنَّمَا ٱلۡعِلۡمُ عِندَ ٱللَّهِ وَإِنَّمَآ أَنَا۠ نَذِيرٞ مُّبِينٞ

    Open ayah 67:26

    Ka ce: “Saninsa yana wurin Allah kawai, kuma ni kawai mai gargaɗi ne mai bayyana (gargaɗin).”

  27. فَلَمَّا رَأَوۡهُ زُلۡفَةٗ سِيٓـَٔتۡ وُجُوهُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَقِيلَ هَٰذَا ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تَدَّعُونَ

    Open ayah 67:27

    To lokacin da za su gan shi a kurkusa, sai fuskokin waɗanda suka kafirce suka yi baƙi, aka kuma ce: “Wannan ne abin da kuka kasance kuna neman zuwansa.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ƙalubalanci kafirai masu bautar wasu gumaka ba Allah ba da zaton za su amfanar da su da cewa, ba su da wata runduna wadda za ta kare su daga azabar Allah idan ya so yi musu azaba, don haka abin da suka runguma a matsayin abin bauta ba Allah ba, ba komai ba ne sai ruɗi irin na Shaiɗan wanda yake yaudarar su yana yi musu ingiza-mai-kantu-ruwa. Ya kuma tabbatar musu cewa, babu wanda zai iya arzuta su idan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya riƙe arzkinsa ya hana su, domin shi ne kaɗai mai arzutawa kuma mai hanawa, sai dai abin da yake faruwa shi ne kafirai sun doge a kan tsaurin kansu da girman kai da fanɗare wa gaskiya. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ba da misalin mumini da kuma kafiri, inda ya bayyana cewa, ba za a taɓa daidaita mushiriki mai bautar wasu gumaka ba Allah ba, yake tafiya a kife a kan fuskarsa ba shi da wata takamaimiyar alƙibla, a haɗa shi da mumini mai kaɗaita Allah wanda yake tafiya a miƙe kyam a kan tafarki madaidaici. Watau duba ga waɗannan mutane biyu kaɗai zai sa a gane babban bambancin da ke tsakaninsu ba tare da an sha wata wahala ba. Hakanan a lahira za a tashi mumini yana tafiya a miƙe kyam a kan miƙaƙƙen tafarki wanda zai kai shi har Aljanna, shi kuma kafiri za a tashe shi yana tafiya a kife a kan fuskarsa bai san inda ya dosa ba har zuwa wutar Jahannama. An karɓo daga Abu Huraira (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Za a tashi mutane a ranar alƙiyama kashi uku; akwai masu tafiya da ƙafafunsu; akwai kuma mahaya ababen hawa; akwai masu tafiya a kan fuskokinsu. Sai sahabbai suka ce: “Ya Manzon Allah, yaya za su riƙa tafiya a kan fuskokinsu?” Sai ya ce: “Wanda ya ba su damar su riƙa tafiya a kan ƙafafunsu shi ne mai ikon ya tafiyar da su a kan fuskokinsu, kuma lalle za su yi ta kauce wa ƙaya da rami da fuskokinsu.” [Ahmad #8647 da Tirmizi #3141]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Annabi (ﷺ) da ya shaida wa mushirikai masu ƙaryata shi cewa lalle Allah shi ne wanda ya halicce su ya ba su kunnuwan da suke ji da su, ya kuma ba su idanu da suke gani da su, ya ba su zukata waɗanda suke fahimta da su. Allah ya yi musu waɗannan ni’imomi ne don su gode masa su bauta masa shi kaɗai, amma sai ga shi kaɗan ne daga cikinsu suke gode masa. Sai kuma Allah ya kuma bayyana musu cewa, shi ne wanda ya halicce su ya kuma baza su a bayan ƙasa, gumakansu kuma ba sa iya halittar komai, don haka su sani cewa zuwa ga Allah ne kaɗai za a tattara su a ranar alƙiyama domin yi musu hisabi da sakamako, gumakansu kuwa ba su da wannan ikon, saboda haka su ji tsoron Allah su bauta masa shi kaɗai ba tare da haɗa shi da wani abokin tarayya ba. Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana tsananin taurin kan mushirikai, domin duk wannan wa’azi da jan hankali da yake yi musu sai ga shi suna tambayar Annabi (ﷺ) da sahabbansa cewa, su faɗa musu yaushe ne alƙawarin tashin alƙiyama zai zo, in har da gaskiya ne alƙiyamar za ta zo? Sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya mayar musu da martani da cewa, sanin zuwan ranar alƙiyama yana ga Allah shi kaɗai, babu wani da ya san sanda za ta zo sai shi, shi kansa Manzon Allah (ﷺ) bai sani ba, domin shi kawai mai bayyana gargaɗi ne a gare su. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, yayin da kafirai za su ga abin da ake yi musu alƙawarinsa na azaba ya zo dab da su, a ranar alƙiyama, to a nan ne fuskokinsu za su canja su yi baƙi ƙirin saboda ɓacin rai da tashin hankali, su kuma mala’iku su yi ta faɗa musu cewa, wannan shi ne abin da suke nema tun a duniya, da a gaggauto musu da shi, to ga shi ya zo kusa da su.

  28. قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِنۡ أَهۡلَكَنِيَ ٱللَّهُ وَمَن مَّعِيَ أَوۡ رَحِمَنَا فَمَن يُجِيرُ ٱلۡكَٰفِرِينَ مِنۡ عَذَابٍ أَلِيمٖ

    Open ayah 67:28

    Ka ce: “Ku ba ni labari, idan Allah Ya hallaka ni da waɗanda suke tare da ni, ko kuma Ya ji ƙan mu, to wane ne zai kare kafirai daga azaba mai raɗaɗi?”

  29. قُلۡ هُوَ ٱلرَّحۡمَٰنُ ءَامَنَّا بِهِۦ وَعَلَيۡهِ تَوَكَّلۡنَاۖ فَسَتَعۡلَمُونَ مَنۡ هُوَ فِي ضَلَٰلٖ مُّبِينٖ

    Open ayah 67:29

    Ka ce: “Shi ne (Allah) Mai rahama, mun yi imani da Shi, kuma a gare Shi muka dogara, to da sannu za ku san shin wane ne yake cikin ɓata mabayyani?”

  30. قُلۡ أَرَءَيۡتُمۡ إِنۡ أَصۡبَحَ مَآؤُكُمۡ غَوۡرٗا فَمَن يَأۡتِيكُم بِمَآءٖ مَّعِينِۭ 

    Open ayah 67:30

    Ka ce: “Ku ba ni labari, idan ruwanku ya wayi gari a ƙafe, to wane ne zai zo muku da ruwa mai ɓuɓɓugowa?” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) ya mayar da martani ga kafirai masu fatan ganin mutuwarsa da abubuwa biyu: <b>Na farko </b>, ya nemi su faɗa masa cewa idan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya karɓi ransa shi da muminai da suke tare da shi ko ya ji ƙan su ya jinkirta musu, to wane amfani za su samu a cikin wannan? Wane ne su kuma zai kuɓutar da su daga azabar Allah mai raɗaɗi idan ta zo musu? Suna tsammanin gumakansu za su amfane su ne? Ko kaɗan babu abin da zai musu amfani idan ba imani da Allah shi kaɗai ba. <b>Na biyu </b>, ya sanar da su cewa, Allah shi ne mai rahama wanda yake kiran su zuwa ga bauta masa shi kaɗai, shi kuma ya yi imani da shi a matsayin abin bauta guda ɗaya, kuma gare shi kaɗai, shi da mabiyansa muminai, suke dogara cikin dukkan al’amuransu, don haka shi ne mai tsare su daga azabar lahira, kuma tabbas ba da jimawa ba za su sani wanda yake cikin ɓata mabayyani ko wanda yake kan tafarki madaidaici, su ne ko shi? Sannan a ayar ƙarshe ta wannan Sura, Allah ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya nemi kafirai su ba shi labari idan aka wayi gari ruwan shansu ya ƙafe ƙaƙaf, to wane ne zai kawo musu wani ruwa mai ɓuɓɓuga a madadinsa, wanda za su riƙa sha suna shuka suna shayar da dabbobinsu? Tabbas babu mai iya yi musu wannan sai Allah shi kaɗai, to me ya hana su dogara gare shi shi kaɗai, su bauta masa ba tare da haɗa shi da abokin tarayya ba?