التحريم

At-Tahrim

The Prohibition · Surah 66 · Ayahs: 12 · Medinan

Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ لِمَ تُحَرِّمُ مَآ أَحَلَّ ٱللَّهُ لَكَۖ تَبۡتَغِي مَرۡضَاتَ أَزۡوَٰجِكَۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

    Open ayah 66:1

    Ya kai wannan Annabi, don me kake haramta abin da Allah Ya halatta maka; kana neman yardar matanka. Allah kuwa Mai gafara ne, Mai jin ƙai.

  2. قَدۡ فَرَضَ ٱللَّهُ لَكُمۡ تَحِلَّةَ أَيۡمَٰنِكُمۡۚ وَٱللَّهُ مَوۡلَىٰكُمۡۖ وَهُوَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡحَكِيمُ

    Open ayah 66:2

    Haƙiƙa Allah Ya farlanta muku kaffarar rantse-rantsenku. Allah kuwa (Shi ne) Majiɓincin al’amarinku, Shi ne kuma Masani, Mai hikima.

  3. وَإِذۡ أَسَرَّ ٱلنَّبِيُّ إِلَىٰ بَعۡضِ أَزۡوَٰجِهِۦ حَدِيثٗا فَلَمَّا نَبَّأَتۡ بِهِۦ وَأَظۡهَرَهُ ٱللَّهُ عَلَيۡهِ عَرَّفَ بَعۡضَهُۥ وَأَعۡرَضَ عَنۢ بَعۡضٖۖ فَلَمَّا نَبَّأَهَا بِهِۦ قَالَتۡ مَنۡ أَنۢبَأَكَ هَٰذَاۖ قَالَ نَبَّأَنِيَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡخَبِيرُ

    Open ayah 66:3

    Kuma (ka tuna) lokacin da Annabi ya asirta wani zance ga wata daga matansa, to lokacin da ta ba da labarinsa Allah kuma Ya bayyana masa shi, sai ya sanar da (ita) sashinsa ya kuma kawar da kai ga wani sashi; to yayin da ya ba ta labarinsa sai ta ce: “Wane ne ya ba ka labarin wannan?” Sai ya ce: “Masani Mai zuzzurfan ilimi ne Ya ba ni labarinsa.”

  4. إِن تَتُوبَآ إِلَى ٱللَّهِ فَقَدۡ صَغَتۡ قُلُوبُكُمَاۖ وَإِن تَظَٰهَرَا عَلَيۡهِ فَإِنَّ ٱللَّهَ هُوَ مَوۡلَىٰهُ وَجِبۡرِيلُ وَصَٰلِحُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۖ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ بَعۡدَ ذَٰلِكَ ظَهِيرٌ

    Open ayah 66:4

    Idan (ku biyun) kuka tuba zuwa ga Allah, to haƙiƙa zukatanku sun riga sun karkata; idan kuwa kuka haɗe masa kai, to lalle Allah Shi ne Majiɓincin al’amarinsa, da Jibrilu da salihan muminai; mala’iku ma bayan wannan masu taimakawa ne.

  5. عَسَىٰ رَبُّهُۥٓ إِن طَلَّقَكُنَّ أَن يُبۡدِلَهُۥٓ أَزۡوَٰجًا خَيۡرٗا مِّنكُنَّ مُسۡلِمَٰتٖ مُّؤۡمِنَٰتٖ قَٰنِتَٰتٖ تَٰٓئِبَٰتٍ عَٰبِدَٰتٖ سَٰٓئِحَٰتٖ ثَيِّبَٰتٖ وَأَبۡكَارٗا

    Open ayah 66:5

    Tabbas idan ya sake ku Ubangijinsa zai musanya masa wasu matan fiye da ku (su zama) Musulmi, muminai, masu biyayya, masu tuba, masu bautar Allah, masu azumi, zawarawa da ‘yanmata. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar da kiran Annabi (ﷺ) da tambayar sa cewa, me ya sa yake haramta wa kansa abin da Allah ya halarta masa, kamar yin saɗaka da kuyangarsa ko shan zuma, don neman yardar matansa masu nuna tsananin kishi. Amma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya gafarta masa, domin shi mai gafara ne mai jin ƙai. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar masa cewa ya shar’anta wa muminai hukuncin warware rantse-rantsensu ta hanyar yin kaffara, idan sun ga cewa aikata abin da suka yi rantsuwa a kan barin sa shi ya fi alheri, ko kuma suka karya rantsuwarsu saboda wani dalili. To su yi kaffara kamar yadda aka yi musu bayani a cikin \'Suratul Ma’ida\', aya ta 89. Allah (Mai tsarki da daukaka) kuma ya bayyana cewa, shi ne majiɓincinsu mai taimakon su kuma masanin halayen da suke ciki da abin da ya fi zame musu maslaha a rayuwarsu, kuma mai hikima ne cikin halittarsa da shari’arsa da Ƙaddararsa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Manzonsa (ﷺ) da ya tuna lokacin da ya keɓance matarsa Hafsa ya sanar da ita wani labari, ya kuma umarce ta da kada ta sanar da kowa wannan labarin, amma sai ta sanar da A’isha, sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sanar da Manzonsa labarin abin da Hafsa ta yi, sai shi kuma ya sanar da ita sashin abin da ta faɗa, ya ɓoye mata wani sashi don cikar haƙurinsa (ﷺ), sai ta tambaye shi cewa, wane ne ya faɗa masa wannan labarin? Sai ya bayyana mata cewa, Allah (Mai tsarki da daukaka) masanin sarari da ɓoye mai zuzzurfan ilimi shi ne ya faɗa masa. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ja hankalin A’isha da Hafsa cewa, lalle su tuba zuwa ga Allah (Mai tsarki da daukaka), domin haƙiƙa zukatansu sun karkata zuwa ga abin da bai dace da su ba, wanda har ya kai ga Manzon Allah (ﷺ) ya haramta wa kansa abin da zuciyarsa take so, don su kuma su ji daɗi; don haka tuba ne ya fi dacewa da su. Amma idan har suka haɗe masa kai a kan abin da yake ƙi, suka ci gaba da irin wannan ɗanyen aiki, to su sani Allah ne majiɓincinsa mai taimakon sa, hakanan Mala’ika Jibirilu da muminai nagari da sauran mala’iku; duka masoyansa ne kuma mataimaka a gare shi. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tsoratar da su cewa, tabbas idan har suka yi musabbabin Annabi (ﷺ) ya sake su, to zai musanya masa su da wasu matayen da suka fi su komai, waɗanda kuma za su zamanto masu miƙa wuya ga umarnin Allah, masu imani da Allah da Manzonsa, masu biyayya ga Allah, masu tuba daga laifukansu, masu bautar Ubangijinsu, masu azumi, zawarawa da ‘yan mata. Sai dai kuma Annabi (ﷺ) bai sake su ba.

  6. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ قُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ وَأَهۡلِيكُمۡ نَارٗا وَقُودُهَا ٱلنَّاسُ وَٱلۡحِجَارَةُ عَلَيۡهَا مَلَٰٓئِكَةٌ غِلَاظٞ شِدَادٞ لَّا يَعۡصُونَ ٱللَّهَ مَآ أَمَرَهُمۡ وَيَفۡعَلُونَ مَا يُؤۡمَرُونَ

    Open ayah 66:6

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ku kare kawunanku da iyalanku daga wuta (wadda) makamashinta mutane ne da duwatsu, masu kula da ita mala’iku ne masu kaushin hali, masu tsananin gaske, ba sa saɓa wa Allah abin da Ya umarce su, suna kuma aikata abin da ake umartar su.

  7. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَا تَعۡتَذِرُواْ ٱلۡيَوۡمَۖ إِنَّمَا تُجۡزَوۡنَ مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ

    Open ayah 66:7

    Ya ku waɗanda suka kafirta, kada ku kawo wani hanzari a yau; ana saka muku ne kawai da abin da kuka kasance kuna aikatawa.

  8. يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ تُوبُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ تَوۡبَةٗ نَّصُوحًا عَسَىٰ رَبُّكُمۡ أَن يُكَفِّرَ عَنكُمۡ سَيِّـَٔاتِكُمۡ وَيُدۡخِلَكُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ يَوۡمَ لَا يُخۡزِي ٱللَّهُ ٱلنَّبِيَّ وَٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مَعَهُۥۖ نُورُهُمۡ يَسۡعَىٰ بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَبِأَيۡمَٰنِهِمۡ يَقُولُونَ رَبَّنَآ أَتۡمِمۡ لَنَا نُورَنَا وَٱغۡفِرۡ لَنَآۖ إِنَّكَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ

    Open ayah 66:8

    Ya ku waɗanda suka yi imani, ku tuba zuwa ga Allah tuba na gaskiya, tabbas Ubangijinku zai kankare muku kurakuranku Ya kuma shigar da ku gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, a ranar da Allah ba zai kunyata Manzo da waɗanda suka yi imani tare da shi ba; haskensu yana tafe a gabansu da damansu suna cewa: “Ya Ubangijinmu, Ka sa haskenmu ya ɗore, Ka kuma gafarta mana; lalle Kai Mai iko ne a kan komai.” A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kira muminai ya umarce su da su kare kawunansu da iyalansu daga shiga wuta, watau ta hanyar sanin umarnin Allah don aiki da shi; da haninsa don guje masa da tuba daga laifuffuka da aikata duk abin da zai jawo wa bawa hushin Allah da azabar wutar Jahannama wadda makamashin hura ta shi ne mutane da duwatsu, kuma masu tsaron ta mala’iku ne masu kaushin hali ga \'yan wuta, ƙarfafa ne masu tsanani, ba sa saɓa wa Allah yayin da ya umarce su, kuma da zarar ya ba su umarni suke zartar da umarninsa ba tare da ɓata lokaci ba. An karɓo daga Abdullahi ɗan Amru (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Annabi (ﷺ) ya ce: “Ku umarci yaro da yin salla idan ya kai shekara bakwai, idan kuma ya kai shekara goma sai ku doke shi a kan barin ta.” [Ahmad #15377 da Abu Dawud #494 da Tirmizi #407]. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, a ranar alƙiyama za a kira waɗanda suka kafirta a shaida musu cewa, kada ma su ce za su kawo wani hanzari game da kafirci da saɓon Allah da suka aikata a duniya, domin faufau ba za a karɓi hanzarinsu ba, saboda lokacin karɓar hanzari ya riga ya wuce tun a duniya, a nan lahira babu abin da za a saka musu da shi sai abin da suka kasance suna aikatawa a duniya na kafirci da saɓon Allah (Mai tsarki da daukaka) da ƙaryata manzannin Allah. Su kuma muminai sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya kira su ya umarce su da su tuba zuwa ga Allah tuba ta gaskiya, domin da haka ne zai kankare musu laifukansu ya kuma shigar da su gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu a ranar alƙiyama, ranar da Allah (Mai tsarki da daukaka) ba zai tozarta Annabi da waɗanda suka yi imani da shi ba, za su zo haskensu yana tafiya a gabansu da damansu, har su tsallake Siraɗi, suna addu’a suna roƙon Allah ya cika musu haskensu har zuwa shigarsu Aljanna. Kada su zama kamar munafukai waɗanda haskensu yake disashewa yayin da suka hau Siraɗi. Suka ci gaba da roƙon Allah da ya gafarta musu zunubansu, domin shi mai iko ne a kan komai, don haka yana iya biya musu dukkan buƙatunsu.

  9. يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ جَٰهِدِ ٱلۡكُفَّارَ وَٱلۡمُنَٰفِقِينَ وَٱغۡلُظۡ عَلَيۡهِمۡۚ وَمَأۡوَىٰهُمۡ جَهَنَّمُۖ وَبِئۡسَ ٱلۡمَصِيرُ

    Open ayah 66:9

    Ya kai wannan Annabi, ka yaƙi kafirai da munafukai, ka kuma tsananta musu. Makomarsu kuma Jahannama ce; makoma kuwa ta munana. A wannan ayar Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi kiran Manzonsa (ﷺ) ya umarce shi da ya yaƙi kafirai da hujjoji da makami, ya kuma yaƙi munafukai da hujjoji, ya kuma tsananta musu a kan haka, ya tsayar musu da hujja da yi musu kyakkyawan wa’azi da rushe ɓarnarsu, da yaƙar duk wanda ya yi taurin kai ya yi ƙoƙarin faɗa da gaskiya ko hana ta yaɗuwa. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar da cewa, kafirai da munafukai duk makomarsu wutar Jahannama ce, kuma lalle wannan makoma tasu ta munana.

  10. ضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ ٱمۡرَأَتَ نُوحٖ وَٱمۡرَأَتَ لُوطٖۖ كَانَتَا تَحۡتَ عَبۡدَيۡنِ مِنۡ عِبَادِنَا صَٰلِحَيۡنِ فَخَانَتَاهُمَا فَلَمۡ يُغۡنِيَا عَنۡهُمَا مِنَ ٱللَّهِ شَيۡـٔٗا وَقِيلَ ٱدۡخُلَا ٱلنَّارَ مَعَ ٱلدَّٰخِلِينَ 

    Open ayah 66:10

    Allah Ya ba da wani misali ga waɗanda suka kafirta da matar Nuhu da matar Luɗu; sun kasance ƙarƙashin (igiyar auren) wasu bayi su biyu salihai daga bayinmu, sai suka ha’ince su, saboda haka ba su wadatar musu komai ba (daga azabar) Allah, aka kuma ce: “Ku shiga wuta tare da masu shiga.”

  11. وَضَرَبَ ٱللَّهُ مَثَلٗا لِّلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱمۡرَأَتَ فِرۡعَوۡنَ إِذۡ قَالَتۡ رَبِّ ٱبۡنِ لِي عِندَكَ بَيۡتٗا فِي ٱلۡجَنَّةِ وَنَجِّنِي مِن فِرۡعَوۡنَ وَعَمَلِهِۦ وَنَجِّنِي مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّٰلِمِينَ

    Open ayah 66:11

    Allah kuma Ya ba da wani misali ga waɗanda suka yi imani da matar Fir’auna lokacin da ta ce: “Ya Ubangijina, Ka gina min gida a wurinka cikin Aljanna, Ka kuma tserar da ni daga Fir’auna da aikinsa, kuma Ka tserar da ni daga azzaluman mutane.”

  12. وَمَرۡيَمَ ٱبۡنَتَ عِمۡرَٰنَ ٱلَّتِيٓ أَحۡصَنَتۡ فَرۡجَهَا فَنَفَخۡنَا فِيهِ مِن رُّوحِنَا وَصَدَّقَتۡ بِكَلِمَٰتِ رَبِّهَا وَكُتُبِهِۦ وَكَانَتۡ مِنَ ٱلۡقَٰنِتِينَ

    Open ayah 66:12

    Da kuma Maryamu ‘yar Imrana wadda ta kiyaye matuncinta, sai Muka masa busa daga Ruhinmu, ta kuma gaskata ayoyin Ubangijinta da littattafansa, ta kuma kasance daga masu biyayya ga Allah. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayar da misalai guda biyu: <b>Na farko </b>, <b> </b>misali ne ga waɗanda suka kafirce wa Allah da Manzanninsa, don su san cewa kusancinsu da alaƙarsu da muminai ba za su amfane su da komai ba a wajen Allah, domin su yi la’akari da matan annabawan nan biyu, watau matar Annabi Nuhu (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da matar Annabi Luɗu, sun kasance matayen aure ne a ƙarƙashin bayin Allah nagari, to amma sai suka ha’ince su, watau suka kafirce musu suka riƙa hana mutane bin addininsu, suka kuma riƙa goyon bayan kafirai maƙiyansu, don haka sai kasancewarsu matan annabawa bai amfana musu komai ba, a ranar lahira kuma za a ce musu, su shiga wutar Jahannama tare da kafirai da fasiƙai masu shigar ta. <b>Misali na biyu </b>, shi ne ga waɗanda suka yi imani da Allah da Manzanninsa, inda ake nuna musu cewa, alaƙarsu ko kusancinsu da kafirai ba zai cutar da su ba matuƙar dai suna tsaye ɗoɗar kan tafarkin Allah madaidaici. Abin la’akari a wajensu shi ne al’amarin matar Fir’auna babban maƙiyin Allah, lokacin da take addu’a tana roƙon Ubangijinta da ya gina mata wani gida a wajensa a Aljanna, ya kuma kuɓutar da ita daga zaluncin Fir’auna da kama-karyarsa da miyagun ayyukansa, ya kuɓutar da ita daga azzaluman mutane masu goyon bayan zaluncin Fir’auna da ta’addancinsa. Sannan kuma ya ba su misali da Maryamu ‘yar Imrana (() wadda ta tsare matuncinta ta kare farjinta daga aikata zina, sai Allah (Mai tsarki da daukaka) ya umarci Mala’ika Jibrilu ya yi busa a cikinsa sai ta sami cikin Annabi Isa (Amincin Allah ya tabbata a gare shi) da Ƙudurar Allah ba tare da uba ba. Ta kuma gaskata shari’o’in Allah da littattafansa da ya saukar wa manzanninsa, ta zamanto daga cikin masu biyayya ga Allah wajen aikata umarninsa da guje wa haninsa. An karɓo daga Abu Musa Al-Ash’ari (Allah ya kara masa yarda) ya ce: Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Maza da yawa sun samu kamala, amma mata ba waɗanda suka samu kamala sai Asiya matar Fir’auna da Maryamu ‘yar Imrana da Khadija ‘yar Khuwailid. Kuma falalar A’isha a kan sauran mata kamar falalar fatan gurasa da romon nama ne a kan sauran abinci.” [Bukhari #3411 da Muslim #2431].