الطلاق
At-Talaaq
Translation: Prof. Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ إِذَا طَلَّقۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَطَلِّقُوهُنَّ لِعِدَّتِهِنَّ وَأَحۡصُواْ ٱلۡعِدَّةَۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ رَبَّكُمۡۖ لَا تُخۡرِجُوهُنَّ مِنۢ بُيُوتِهِنَّ وَلَا يَخۡرُجۡنَ إِلَّآ أَن يَأۡتِينَ بِفَٰحِشَةٖ مُّبَيِّنَةٖۚ وَتِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِۚ وَمَن يَتَعَدَّ حُدُودَ ٱللَّهِ فَقَدۡ ظَلَمَ نَفۡسَهُۥۚ لَا تَدۡرِي لَعَلَّ ٱللَّهَ يُحۡدِثُ بَعۡدَ ذَٰلِكَ أَمۡرٗا
Open ayah 65:1<b>Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin ƙai </b> 1. Ya kai wannan Annabi, (ka ce da jama’arka): “Idan za ku saki mata sai ku sake su a farkon iddarsu, ku kuma kula da ƙidaya idda; kuma ku kiyaye dokokin Ubangijinku; kada ku fitar da su daga ɗakunansu, su ma kada su fita sai dai idan sun aikata alfasha bayayyananna. Waɗannan kuwa su ne iyakokin Allah. Wanda kuwa duk ya ƙetare iyakokin Allah, to haƙiƙa ya zalunci kansa. Ba ka sani ba ko Allah zai farar da wani al’amari bayan wannan. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya buɗe wannan Surar da kiran Annabi (ﷺ) ya ba shi umarni shi da al’ummarsa cewa, idan suka tashi sakin matansu na aure to su sake su a farkon iddarsu, watau lokacin da suka yi tsarkin haila wanda kuma ba su sadu da su ba a cikinsa, sannan ya umarce su da su kula da ƙidayar kwanakin iddar, domin su iya dawo da matansu kafin ƙarewarta idan suna da buƙatar yin haka. Ya kuma umarce su da su kiyaye dokokinsa, su yi aiki da umarninsa, su kuma guji haninsa. An karɓo daga Abdurrahman ɗan Aiman ya ce: Na tambayi Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) cewa: “Me kake gani game da mutumin da ya saki matarsa tana haila?” Sai ya ce: “Ibnu Umar ya saki matarsa tana haila a zamanin Manzon Allah (ﷺ), sai Umar (Allah ya kara masa yarda) ya tambayi Manzon Allah a kan haka, ya ce masa: Abdullahi ɗan Umar ya saki matarsa tana haila”, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa: “Lalle ya dawo da ita”. Sai ya dawo da ita. Manzon Allah (ﷺ) ya ce masa: “Idan ta yi tsarki to yana iya ya sake ta, ko ya riƙe ta.” Ibn Umar ya ce: Sai Annabi (ﷺ) ya karanta wannan ayar. [Muslim #1471]. An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (Allah ya kara masa yarda) cewa, ya saki matarsa tana al’ada a zamanin Annabi (ﷺ), sai Umar ɗan Khaɗɗabi (Allah ya kara masa yarda) ya yi wa Annabi (ﷺ) tambaya a kan haka. Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Ka umarce shi ya dawo da ita, sannan ya riƙe ta har sai ta yi tsarki, sannan ta yi haila, sannan ta yi wani tsarkin, sannan idan ya ga dama sai ya riƙe ta, idan kuma ya ga dama sai ya sake ta tun gabanin ya kusance ta, to wannan ita ce iddar da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi umarni a saki mata a cikinta.” [Bukhari #5251 da Muslim #1471]. Sannan lokacin da matan da suka saki suke zaune a gidajensu suna yin idda, to kada su fitar da su daga gidajensu, su ma kuma matan kada su fice da kansu har sai sun gama iddarsu. Amma wannan da sharaɗin kada su matayen su zo da wani mummunan aiki a gidajen, watau kamar zina ko cin mutuncin mutanen gidan, to idan haka ya faru ya halatta a kore su ko a fitar da su, don tsayar musu da hukuncin Allah. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi gargaɗi da cewa waɗannan hukunce-hukunce da ya bayyana musu iyakokin Allah ne, duk kuwa wanda ya kuskura ya tsallake iyakokinsa, to lalle ya cuci kansa, domin ya jefa kansa cikin hushin Allah da azabarsa. Kuma Allah ya bayyana musu hikimar da ta sa ya hana su fitar da matansu da suka saki daga gidajensu, ko su matan su fice da kansu da cewa, mai yiwuwa ne Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake kawo jituwa a tsakanin mijin da matar, su fahimci matsalolinsu, su mayar da aurensu ya ci gaba.
فَإِذَا بَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَأَمۡسِكُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٍ أَوۡ فَارِقُوهُنَّ بِمَعۡرُوفٖ وَأَشۡهِدُواْ ذَوَيۡ عَدۡلٖ مِّنكُمۡ وَأَقِيمُواْ ٱلشَّهَٰدَةَ لِلَّهِۚ ذَٰلِكُمۡ يُوعَظُ بِهِۦ مَن كَانَ يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۚ وَمَن يَتَّقِ ٱللَّهَ يَجۡعَل لَّهُۥ مَخۡرَجٗا
Open ayah 65:2Idan kuma sun kusa isa ƙarshen iddarsu, to ku riƙe su da kyautatawa (ku yi kome), ko kuma ku rabu da su da kyautatawa, kuma ku kafa shaidar adilai guda biyu daga cikinku, ku kuma tsayar da shaidarku saboda Allah. Wannan shi ne ake yin wa’azi da shi ga wanda ya kasance yana yin imani da Allah da ranar lahira. Wanda kuma ya kiyaye dokokin Allah to zai sanya masa mafita.
وَيَرۡزُقۡهُ مِنۡ حَيۡثُ لَا يَحۡتَسِبُۚ وَمَن يَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱللَّهِ فَهُوَ حَسۡبُهُۥٓۚ إِنَّ ٱللَّهَ بَٰلِغُ أَمۡرِهِۦۚ قَدۡ جَعَلَ ٱللَّهُ لِكُلِّ شَيۡءٖ قَدۡرٗا
Open ayah 65:3Ya kuma arzuta shi ta inda ba ya tsammani. Duk wanda kuma ya dogara ga Allah to Shi Ya ishe shi. Lalle Allah Mai zartar da al\'amarinsa ne. Haƙiƙa kuma Allah Ya sanya iyaka ga kowane abu. A waɗannan ayoyi kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya ci gaba da sanar da muminai hukunce-hukuncen saki da kome, da jan hankalinsu a kan su kiyaye dokokinsa don su sami mafita a cikin al’amuransu. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa, idan matan da suka yi wa saki na ɗaya ko na biyu suka kusa gama iddarsu, to suna da ɗayan zaɓi guda biyu: 1. Ko dai su yi musu kome idan suna son su riƙe su da kyautatawa da mutuntawa da kulawa da haƙƙoƙinsu. 2. Ko kuma su rabu da su har su ƙare iddarsu ba tare da tsangwama ko matsanta musu ba, tare kuma da ba su cikakakkun haƙƙoƙinsu, ko ma su kyautata musu da wani abin ihsani don rage musu zafin raɗaɗin rabuwa da kuma surutan mutane. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi umarni idan maza za su yi kome ko za su rabu da matansu to su kafa shaidu biyu adalai a kan sakin ko komen, domin kauce wa duk wani saɓani ko rikici a gaba. Sannan ya umarci su ma masu bayar da shaida da su tsayar da shaidarsu a kan gaskiya tare da neman yardar Allah, watau kada su rage ko su ƙara a kan abin da suka sani. Sai kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya nuna wa muminai cewa, waɗannan hukunce-hukunce da iyakoki da yake bayyana musu, yana yin haka ne don su zamanto wa’azi ga wanda ya yi imani da Allah da ranar alƙiyama, domin shi ne kawai wanda zai amfana da tunatarwa da wa’azi. Kuma Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi musu alƙawari da cewa, duk wanda ya tsare dokokinsa, ya yi aiki da umarninsa ya guje wa haninsa, to lalle zai sanya masa mafita daga duk wani ƙunci ko damuwa da zai faɗa cikinta, kuma zai arzuta shi ta inda ba ya tsammani. Don haka mumini ya ci gaba da dogaro ga Allah da mayar da al’amuransa a gare shi, domin ya yi alƙawarin cewa, duk wanda ya dogara gare shi cikin al’amuransa, to shi ya ishe shi ga komai, kuma Allah shi ne mai zartar da al’amarinsa yadda ya ga dama, babu mai iya hana shi, ko wani abu ya gagare shi. Allah ya riga ya sanya wa komai iyaka da yake tuƙewa zuwa gare ta, don haka tsanani yana da iyaka, jin daɗi ma yana da iyaka, babu wani abu mai dawwama har abada a nan duniya.
وَٱلَّٰٓـِٔي يَئِسۡنَ مِنَ ٱلۡمَحِيضِ مِن نِّسَآئِكُمۡ إِنِ ٱرۡتَبۡتُمۡ فَعِدَّتُهُنَّ ثَلَٰثَةُ أَشۡهُرٖ وَٱلَّٰٓـِٔي لَمۡ يَحِضۡنَۚ وَأُوْلَٰتُ ٱلۡأَحۡمَالِ أَجَلُهُنَّ أَن يَضَعۡنَ حَمۡلَهُنَّۚ وَمَن يَتَّقِ ٱللَّهَ يَجۡعَل لَّهُۥ مِنۡ أَمۡرِهِۦ يُسۡرٗا
Open ayah 65:4Waɗanda kuma suka ɗebe ƙauna ta yin al’ada daga matanku, idan kun yi kokwanto, to iddarsu wata uku ne, da kuma waɗanda ba su taɓa yin al’ada ba. Mata masu ciki kuma ƙarewar iddarsu ita ce haife cikinsu. Duk kuma wanda ya kiyaye dokokin Allah, to zai sanya masa sauƙi game da al’amarinsa
ذَٰلِكَ أَمۡرُ ٱللَّهِ أَنزَلَهُۥٓ إِلَيۡكُمۡۚ وَمَن يَتَّقِ ٱللَّهَ يُكَفِّرۡ عَنۡهُ سَيِّـَٔاتِهِۦ وَيُعۡظِمۡ لَهُۥٓ أَجۡرًا
Open ayah 65:5Wannan shi ne hukuncin Allah da Ya saukar da shi a gare ku. Duk kuma wanda ya kiyaye dokokin Allah, to zai kankare masa zunubbansa Ya kuma girmama masa lada. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana iddar wasu nau’ikan mata guda uku: <b>Na ɗaya, </b> matan da suka manyanta har suka cire tsammani daga yin jinin haila, idan ana tantama game da iddarsu, to iddarsu wata uku ne cur. <b>Na biyu, </b> yara mata ƙanana waɗanda ba su fara yin jinin haila ba, to su ma iddarsu ta saki wata uku ne cikakku. <b>Na uku, </b>su ne matan da aka sake su ko mazajensu suka rasu suka bar su da ciki, to iddarsu ita ce su haife abin da yake cikinsu, da zarar ta haihu to ta fita daga idda ko takaba ke nan. An karɓo daga Ummu Salama (Allah ya kara mata yarda) ta ce: An kashe mijin Subai’atul Aslamiyya alhalin tana da ciki, sai ta haihu bayan mutuwarsa da kwana arba’in, sai aka fito neman aurenta, sai Manzon Allah (ﷺ) ya aurar da ita. [Bukhari #4909 da Muslim #1484]. Sannan Allah (Mai tsarki da daukaka) ya sake tabbatar wa muminai cewa, duk wanda ya kiyaye dokokinsa, to zai sanya masa sauƙi game da al’amarinsa. Ya kuma bayyana musu cewa, wannan hukunci da ya ambata na saki da kome da idda hukuncin Allah ne da ya saukar musu, don su yi aiki da shi, su kiyaye dokokinsa da ya kafa musu; duk kuwa wanda ya kiyaye dokokin Allah, ya yi aiki da umarninsa ya guje wa haninsa, to zai kankare masa laifukansa, ya kuma ba shi lada mai girma a lahira, shi ne shiga Aljanna da samun jin daɗi na har abada.
أَسۡكِنُوهُنَّ مِنۡ حَيۡثُ سَكَنتُم مِّن وُجۡدِكُمۡ وَلَا تُضَآرُّوهُنَّ لِتُضَيِّقُواْ عَلَيۡهِنَّۚ وَإِن كُنَّ أُوْلَٰتِ حَمۡلٖ فَأَنفِقُواْ عَلَيۡهِنَّ حَتَّىٰ يَضَعۡنَ حَمۡلَهُنَّۚ فَإِنۡ أَرۡضَعۡنَ لَكُمۡ فَـَٔاتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ وَأۡتَمِرُواْ بَيۡنَكُم بِمَعۡرُوفٖۖ وَإِن تَعَاسَرۡتُمۡ فَسَتُرۡضِعُ لَهُۥٓ أُخۡرَىٰ
Open ayah 65:6Ku zaunar da su (matayen) a inda kuka zauna daidai da samunku, kada kuma ku cuce su don ku ƙuntata musu. Idan kuwa sun kasance masu ciki to sai ku ciyar da su har sai sun haife cikinsu. Sannan idan sun shayar muku da (‘ya’yanku) sai ku ba su ladansu; ku kuma daidaita a tsakaninku ta hanya tagari; idan kuma kuka kasa daidaitawa, to wata mai shayarwar sai ta shayar masa.
لِيُنفِقۡ ذُو سَعَةٖ مِّن سَعَتِهِۦۖ وَمَن قُدِرَ عَلَيۡهِ رِزۡقُهُۥ فَلۡيُنفِقۡ مِمَّآ ءَاتَىٰهُ ٱللَّهُۚ لَا يُكَلِّفُ ٱللَّهُ نَفۡسًا إِلَّا مَآ ءَاتَىٰهَاۚ سَيَجۡعَلُ ٱللَّهُ بَعۡدَ عُسۡرٖ يُسۡرٗا
Open ayah 65:7Mawadaci ya ciyar daidai da wadatarsa; wanda kuwa aka ƙuntata masa arzikinsa, to ya ciyar daidai da abin da Allah Ya ba shi. Allah ba Ya ɗora wa rai sai gwargwadon abin da Ya ba shi. Kuma da sannu Allah zai sanya sauƙi bayan tsanani. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi bayanin hukuncin ba wa matan da aka saka saki na farko ko na biyu wurin zama, inda ya umarci mazaje da su ba su wurin zama gwargwadon samunsu, Allah bai ɗora musu abin da ya fi ƙarfinsu ba, kada kuma su cutar da su game da ciyarwa ko ba su matsuguni, don su ƙuntata musu har su sanya su bar gidajen ba don suna so ba. Sai kuma ya bayyana haƙƙin ciyar da matar da aka saka tana da ciki, ya yi umarni da a ciyar da su har sai sun haife abin da yake cikinsu. Sannan bayan sun haifi ‘ya’yansu, to idan sun shayar da su, sai mazajensu su biya su ladan shayarwarsu, kuma yana da kyau uban da uwar ɗansa da suka rabu su tattauna game da ladan da zai riƙa biya na shayar da ɗansa ta hanyar da ta dace wadda babu ƙwaruwa ga matar ko mijin a ciki. Idan aka yi rashin dace shi mijin ya matse hannu ya yi rowar ladan da ya kamata ya biya na shayar masa da ɗansa, ita ma kuma ta dage sai an biya ta abin da ta yanka, to sai uban ya nemo wata mai shayarwar da za ta shayar masa da ɗansa. Sai kuma game da batun ciyarwa, Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana cewa, kowa za a dubi gwargwadon wadatarsa ko talaucinsa, idan miji mai wadata ne sai ya ciyar da sakakkiyar matarsa da ɗansa gwargwadon wadatarsa, wanda kuma yake mai ƙaramin ƙarfi ne, shi ma sai ya ciyar gwargwadon abin da Allah (Mai tsarki da daukaka) ya hore masa, domin ba wani mutum da Allah yake ɗora masa abin da ya fi ƙarfinsa. Sannan mutane su sani cewa komai na Allah ne, bayan duk wani tsanani yakan kawo sauƙi, ya hore wa talaka arziki mai yawa da wadata.
وَكَأَيِّن مِّن قَرۡيَةٍ عَتَتۡ عَنۡ أَمۡرِ رَبِّهَا وَرُسُلِهِۦ فَحَاسَبۡنَٰهَا حِسَابٗا شَدِيدٗا وَعَذَّبۡنَٰهَا عَذَابٗا نُّكۡرٗا
Open ayah 65:8Alƙaryu da dama sun yi wa Ubangijinsu da manzanninsa taurin kai, sai Muka yi musu hisabi mai tsanani, Muka azabtar da su azaba mummuna.
فَذَاقَتۡ وَبَالَ أَمۡرِهَا وَكَانَ عَٰقِبَةُ أَمۡرِهَا خُسۡرًا
Open ayah 65:9Saboda haka su ɗanɗani ƙarshen al’amarinsu, ƙarshen al’amarin nasu kuma ya zama taɓewa.
أَعَدَّ ٱللَّهُ لَهُمۡ عَذَابٗا شَدِيدٗاۖ فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ يَٰٓأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْۚ قَدۡ أَنزَلَ ٱللَّهُ إِلَيۡكُمۡ ذِكۡرٗا
Open ayah 65:10Allah Ya tanadar musu azaba mai tsanani; saboda haka ku kiyaye dokokin Allah ya ku ma’abota hankula waɗanda suka yi imani. Haƙiƙa Allah Ya saukar muku da tunatarwa.
رَّسُولٗا يَتۡلُواْ عَلَيۡكُمۡ ءَايَٰتِ ٱللَّهِ مُبَيِّنَٰتٖ لِّيُخۡرِجَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ مِنَ ٱلظُّلُمَٰتِ إِلَى ٱلنُّورِۚ وَمَن يُؤۡمِنۢ بِٱللَّهِ وَيَعۡمَلۡ صَٰلِحٗا يُدۡخِلۡهُ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُ خَٰلِدِينَ فِيهَآ أَبَدٗاۖ قَدۡ أَحۡسَنَ ٱللَّهُ لَهُۥ رِزۡقًا
Open ayah 65:11(Shi ne) Manzo da yake karanta muku ayoyin Allah bayyanannu, don ya fitar da waɗanda suka yi imani suka kuma yi aiki nagari daga duffai zuwa haske. Duk kuwa wanda ya yi imani da Allah ya kuma yi aiki nagari to zai shigar da shi gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu suna masu dawwama a cikinsu har abada. (Wanda aka yi wa haka kuwa) haƙiƙa Allah Ya kyautata masa arzikinsa. A waɗannan ayoyi Allah (Mai tsarki da daukaka) ya yi gargaɗi ne game da bijire wa umarninsa da watsi da hukunce-hukuncensa, inda ya bayyana cewa, alƙaryu da dama waɗanda suka bijire wa bin umarnin Ubangijinsu suka saɓa wa manzanninsa, ya yi musu hisabi mai tsanani da mummunar azaba a kan miyagun ayyukansu a nan duniya kafin abin da yake jiran su a lahira, don haka suka ɗanɗani uƙubar munanan ayyukansu waɗanda ƙarshensu ya zamanto asara ce ta duniya da lahira. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya tabbatar musu cewa, ya yi musu tanadin azaba mai tsanani da take jiran su a kan kafircinsu da taurin kansu ga manzanninsa, don haka Allah ya umarci muminai masu hankali waɗanda suka yi imani da shi da Manzonsa (ﷺ) da su kiyaye dokokinsa, su yi aiki da umarninsa, su kuma guje wa munanan ayyuka, kada su yi sake har azabar da ta sauka a kan al’ummun da suka gabace su su ma ta sauka a kansu; kuma su tuna da cewa lalle Allah (Mai tsarki da daukaka) ya saukar musu da Alƙur’ani wanda yake tunatar da su mummunan ƙarshen mai saɓon Allah da kyakkyawan ƙarshen mutane nagari. Allah (Mai tsarki da daukaka) ya bayyana musu cewa, wannan tunatarwa kuwa ita ce Alƙur’ani wanda Manzonsa (ﷺ) ya zo yana karanta musu ayoyinsa bayyanannu waɗanda babu wata rikitarwa a cikinsu, domin ya fitar da waɗanda suka yi imani da shi kuma suka yi ayyuka nagari daga duffan ɓata zuwa ga hasken shiriya. Duk kuwa wanda ya yi imani da Allah ya yi kyakkywan aiki, to Allah zai shigar da su gidajen Aljanna waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har abada. Tabbas duk wannan Allah ya kyautata masa arzikinsa har ya shigar da shi gidan Aljannar da ni’imarta ba mai yankewa ba ce har abada, to wannan ya rabauta.
ٱللَّهُ ٱلَّذِي خَلَقَ سَبۡعَ سَمَٰوَٰتٖ وَمِنَ ٱلۡأَرۡضِ مِثۡلَهُنَّۖ يَتَنَزَّلُ ٱلۡأَمۡرُ بَيۡنَهُنَّ لِتَعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ قَدِيرٞ وَأَنَّ ٱللَّهَ قَدۡ أَحَاطَ بِكُلِّ شَيۡءٍ عِلۡمَۢا
Open ayah 65:12Allah ne Wanda Ya halicci sammai bakwai, ƙasa ma Ya halicci kwatankwacinsu (watau sammai), umarni yana sauka a tsakaninsu, don ku san cewa, Allah Mai iko ne a kan komai, kuma haƙiƙa Allah iliminsa ya kewaye kowane abu. A wannan aya ta ƙarshe Allah (Mai tsarki da daukaka) ya rufe magana a kan dokokinsa da hukunce-hukuncensa na aure da bayanin girman Ƙudurarsa da faffaɗan iliminsa da cewa, shi ne ya halicci sammai bakwai da ƙassai bakwai kamar adadin sammai. Umarninsa na shari’a da na halitta yana saukowa daga tsakaninsu, kuma ya yi haka ne don bayinsa su san cewa, iliminsa ya kewaye komai, babu wani abu a sama ko a ƙasa da bai san shi ba. Watau idan bayi suka san Allah da mafi kyan sunayensu da mafi ɗaukakar siffofinsa masu tsarki, sai su so shi, su bauta masa, su kula da haƙƙoƙinsa, wannan kuwa shi ne babban maƙasudin halittarsu da saukar musu da shari’u.