القيامة
Al-Qiyaama
Translation: Hausa - Abubakar Mahmoud Gumi · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
لَآ أُقۡسِمُ بِيَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ
Open ayah 75:1Bã sai Nã yi rantsuwa da Rãnar ¡iyãma ba.
وَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلنَّفۡسِ ٱللَّوَّامَةِ
Open ayah 75:2Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin kansa ba.
أَيَحۡسَبُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَلَّن نَّجۡمَعَ عِظَامَهُۥ
Open ayah 75:3Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba?
بَلَىٰ قَٰدِرِينَ عَلَىٰٓ أَن نُّسَوِّيَ بَنَانَهُۥ
Open ayah 75:4Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa.
بَلۡ يُرِيدُ ٱلۡإِنسَٰنُ لِيَفۡجُرَ أَمَامَهُۥ
Open ayah 75:5Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa.
يَسۡـَٔلُ أَيَّانَ يَوۡمُ ٱلۡقِيَٰمَةِ
Open ayah 75:6Yanã tambaya: ";Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?";
فَإِذَا بَرِقَ ٱلۡبَصَرُ
Open ayah 75:7To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli).
وَخَسَفَ ٱلۡقَمَرُ
Open ayah 75:8Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe).
وَجُمِعَ ٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُ
Open ayah 75:9Aka tãra rãnã da watã
يَقُولُ ٱلۡإِنسَٰنُ يَوۡمَئِذٍ أَيۡنَ ٱلۡمَفَرُّ
Open ayah 75:10Mutum zai ce a rãn nan ";Ina wurin gudu?";
كَلَّا لَا وَزَرَ
Open ayah 75:11A'aha! bãbu mafaka.
إِلَىٰ رَبِّكَ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡمُسۡتَقَرُّ
Open ayah 75:12zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake.
يُنَبَّؤُاْ ٱلۡإِنسَٰنُ يَوۡمَئِذِۭ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ
Open ayah 75:13Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar.
بَلِ ٱلۡإِنسَٰنُ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦ بَصِيرَةٞ
Open ayah 75:14Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne.
وَلَوۡ أَلۡقَىٰ مَعَاذِيرَهُۥ
Open ayah 75:15Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba).
لَا تُحَرِّكۡ بِهِۦ لِسَانَكَ لِتَعۡجَلَ بِهِۦٓ
Open ayah 75:16Kada ka mõtsar da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni).
إِنَّ عَلَيۡنَا جَمۡعَهُۥ وَقُرۡءَانَهُۥ
Open ayah 75:17Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa.
فَإِذَا قَرَأۡنَٰهُ فَٱتَّبِعۡ قُرۡءَانَهُۥ
Open ayah 75:18To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa.
ثُمَّ إِنَّ عَلَيۡنَا بَيَانَهُۥ
Open ayah 75:19sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa.
كَلَّا بَلۡ تُحِبُّونَ ٱلۡعَاجِلَةَ
Open ayah 75:20A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne.
وَتَذَرُونَ ٱلۡأٓخِرَةَ
Open ayah 75:21Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira).
وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ نَّاضِرَةٌ
Open ayah 75:22Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne.
إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٞ
Open ayah 75:23Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne.
وَوُجُوهٞ يَوۡمَئِذِۭ بَاسِرَةٞ
Open ayah 75:24Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne.
تَظُنُّ أَن يُفۡعَلَ بِهَا فَاقِرَةٞ
Open ayah 75:25Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso.
كَلَّآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلتَّرَاقِيَ
Open ayah 75:26A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai.
وَقِيلَ مَنۡۜ رَاقٖ
Open ayah 75:27kuma aka ce: ";Wãne ne mai tawada?";
وَظَنَّ أَنَّهُ ٱلۡفِرَاقُ
Open ayah 75:28Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce.
وَٱلۡتَفَّتِ ٱلسَّاقُ بِٱلسَّاقِ
Open ayah 75:29Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri.
إِلَىٰ رَبِّكَ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡمَسَاقُ
Open ayah 75:30Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa take.
فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّىٰ
Open ayah 75:31To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba!
وَلَٰكِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ
Open ayah 75:32Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya!
ثُمَّ ذَهَبَ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ يَتَمَطَّىٰٓ
Open ayah 75:33Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama.
أَوۡلَىٰ لَكَ فَأَوۡلَىٰ
Open ayah 75:34Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa.
ثُمَّ أَوۡلَىٰ لَكَ فَأَوۡلَىٰٓ
Open ayah 75:35Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa.
أَيَحۡسَبُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَن يُتۡرَكَ سُدًى
Open ayah 75:36Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)?
أَلَمۡ يَكُ نُطۡفَةٗ مِّن مَّنِيّٖ يُمۡنَىٰ
Open ayah 75:37Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa)
ثُمَّ كَانَ عَلَقَةٗ فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ
Open ayah 75:38Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa;
فَجَعَلَ مِنۡهُ ٱلزَّوۡجَيۡنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰٓ
Open ayah 75:39Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace?
أَلَيۡسَ ذَٰلِكَ بِقَٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يُحۡـِۧيَ ٱلۡمَوۡتَىٰ
Open ayah 75:40Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu?