المدثر
Al-Muddaththir
Translation: Hausa - Abubakar Mahmoud Gumi · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡمُدَّثِّرُ
Open ayah 74:1Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi.
قُمۡ فَأَنذِرۡ
Open ayah 74:2Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi
وَرَبَّكَ فَكَبِّرۡ
Open ayah 74:3Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi,
وَثِيَابَكَ فَطَهِّرۡ
Open ayah 74:4Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su,
وَٱلرُّجۡزَ فَٱهۡجُرۡ
Open ayah 74:5Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu.
وَلَا تَمۡنُن تَسۡتَكۡثِرُ
Open ayah 74:6Kada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri
وَلِرَبِّكَ فَٱصۡبِرۡ
Open ayah 74:7Kuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure
فَإِذَا نُقِرَ فِي ٱلنَّاقُورِ
Open ayah 74:8To, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho.
فَذَٰلِكَ يَوۡمَئِذٖ يَوۡمٌ عَسِيرٌ
Open ayah 74:9To, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya
عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ غَيۡرُ يَسِيرٖ
Open ayah 74:10A kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne.
ذَرۡنِي وَمَنۡ خَلَقۡتُ وَحِيدٗا
Open ayah 74:11Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai,
وَجَعَلۡتُ لَهُۥ مَالٗا مَّمۡدُودٗا
Open ayah 74:12Kuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya
وَبَنِينَ شُهُودٗا
Open ayah 74:13Da ɗiyã halartattu,
وَمَهَّدتُّ لَهُۥ تَمۡهِيدٗا
Open ayah 74:14Kuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa.
ثُمَّ يَطۡمَعُ أَنۡ أَزِيدَ
Open ayah 74:15Sa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri!
كَلَّآۖ إِنَّهُۥ كَانَ لِأٓيَٰتِنَا عَنِيدٗا
Open ayah 74:16Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyinMu, mai tsaurin kai.
سَأُرۡهِقُهُۥ صَعُودًا
Open ayah 74:17Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa.
إِنَّهُۥ فَكَّرَ وَقَدَّرَ
Open ayah 74:18Lalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur'ãni)
فَقُتِلَ كَيۡفَ قَدَّرَ
Open ayah 74:19Sabõda haka, aka la'ane shi, kamar yadda ya ƙaddara.
ثُمَّ قُتِلَ كَيۡفَ قَدَّرَ
Open ayah 74:20Sa'an nan, aka la'ane shi kamar yadda ya ƙaddara.
ثُمَّ نَظَرَ
Open ayah 74:21Sa'an nan, ya yi tunãni
ثُمَّ عَبَسَ وَبَسَرَ
Open ayah 74:22Sa'an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk.
ثُمَّ أَدۡبَرَ وَٱسۡتَكۡبَرَ
Open ayah 74:23Sa'an nan, ya jũya bãya, kuma ya bunƙãsa,
فَقَالَ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٞ يُؤۡثَرُ
Open ayah 74:24Sai ya ce: ";Wannan abu dai bã kõme ba ne fãce wani sihiri, wanda aka ruwaito.";
إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا قَوۡلُ ٱلۡبَشَرِ
Open ayah 74:25";Wannan maganar mutum dai ce.";
سَأُصۡلِيهِ سَقَرَ
Open ayah 74:26Zã Ni ƙõna shi da Saƙar.
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا سَقَرُ
Open ayah 74:27Kuma mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽwa Saƙar!
لَا تُبۡقِي وَلَا تَذَرُ
Open ayah 74:28Bã ta ragẽwa, kuma bã ta bari.
لَوَّاحَةٞ لِّلۡبَشَرِ
Open ayah 74:29Mai nãcẽwa ga jiki ce (da (ƙũna).
عَلَيۡهَا تِسۡعَةَ عَشَرَ
Open ayah 74:30A kanta akwai (matsara) gõma shã tara.
وَمَا جَعَلۡنَآ أَصۡحَٰبَ ٱلنَّارِ إِلَّا مَلَٰٓئِكَةٗۖ وَمَا جَعَلۡنَا عِدَّتَهُمۡ إِلَّا فِتۡنَةٗ لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ لِيَسۡتَيۡقِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَيَزۡدَادَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِيمَٰنٗا وَلَا يَرۡتَابَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَلِيَقُولَ ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٞ وَٱلۡكَٰفِرُونَ مَاذَآ أَرَادَ ٱللَّهُ بِهَٰذَا مَثَلٗاۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ ٱللَّهُ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُۚ وَمَا يَعۡلَمُ جُنُودَ رَبِّكَ إِلَّا هُوَۚ وَمَا هِيَ إِلَّا ذِكۡرَىٰ لِلۡبَشَرِ
Open ayah 74:31Kuma ba Mu sanya ma'abũta wutã (wãto matsaranta) ba, fãce malã'iku, kuma ba Mu sanya adadinsu (gõma sha tara) ba, fãce dõmin fitina ga waɗanda suka kãfirta domin waɗanda aka bai wa littãfi su sãmi yaƙĩni kuma waɗanda suka yi ĩmãni su ƙãra ĩmãni, kuma waɗanda aka bai wa littãfi da mũminai bã zã su yi shakka ba, kuma domin wa ɗanda a cikin zukatansu akwai wata cuta da kãfirai su ce: ";Mẽ Allah Yake nufi da wannan, ya kasance misãli?"; Haka dai Allah ke ɓatar da wanda Ya so, kuma Ya shiryar da wanda ya so. Kuma bãbu wanda ya san mayãƙan Ubangijinka fãce Shi, kuma ita (wutar) ba ta kasance ba fãce wata tunãtarwa ce ga mutum.
كَلَّا وَٱلۡقَمَرِ
Open ayah 74:32A'aha! Ina rantsuwa da watã.
وَٱلَّيۡلِ إِذۡ أَدۡبَرَ
Open ayah 74:33Da dare a lõkacin da ya jũyar da baya.
وَٱلصُّبۡحِ إِذَآ أَسۡفَرَ
Open ayah 74:34Da sãfiya idan ta wãye.
إِنَّهَا لَإِحۡدَى ٱلۡكُبَرِ
Open ayah 74:35Ita (wutar) ɗayan manyan masĩfũ? ce.
نَذِيرٗا لِّلۡبَشَرِ
Open ayah 74:36Mai gargaɗĩ ce ga mutum.
لِمَن شَآءَ مِنكُمۡ أَن يَتَقَدَّمَ أَوۡ يَتَأَخَّرَ
Open ayah 74:37Ga wanda ya so, daga cikinku, ya gabãta ko ya jinkirta.
كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡ رَهِينَةٌ
Open ayah 74:38Kõwane rai ga abin da ya aikata jingina ce.
إِلَّآ أَصۡحَٰبَ ٱلۡيَمِينِ
Open ayah 74:39Fãce mutãnen dãma.
فِي جَنَّٰتٖ يَتَسَآءَلُونَ
Open ayah 74:40A cikin Aljanna suna tambayar jũna.
عَنِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ
Open ayah 74:41Game da mãsu laifi.
مَا سَلَكَكُمۡ فِي سَقَرَ
Open ayah 74:42(Su ce musu) ";Me ya shigar da ku a cikin Saƙar?";
قَالُواْ لَمۡ نَكُ مِنَ ٱلۡمُصَلِّينَ
Open ayah 74:43Suka ce: ";Ba mu kasance munã a cikin mãsu salla ba.";
وَلَمۡ نَكُ نُطۡعِمُ ٱلۡمِسۡكِينَ
Open ayah 74:44";Kuma ba mu kasance muna ciyar da matalautã ba.";
وَكُنَّا نَخُوضُ مَعَ ٱلۡخَآئِضِينَ
Open ayah 74:45";Kuma mun kasance muna kũtsãwa tãre da mãsu kũtsãwa.";
وَكُنَّا نُكَذِّبُ بِيَوۡمِ ٱلدِّينِ
Open ayah 74:46";Mun kasance munã ƙaryata rãnar sãkamako.";
حَتَّىٰٓ أَتَىٰنَا ٱلۡيَقِينُ
Open ayah 74:47";Har gaskiya (wãto mutuwa) ta zo mana.";
فَمَا تَنفَعُهُمۡ شَفَٰعَةُ ٱلشَّٰفِعِينَ
Open ayah 74:48Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba.
فَمَا لَهُمۡ عَنِ ٱلتَّذۡكِرَةِ مُعۡرِضِينَ
Open ayah 74:49Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya.
كَأَنَّهُمۡ حُمُرٞ مُّسۡتَنفِرَةٞ
Open ayah 74:50Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne.
فَرَّتۡ مِن قَسۡوَرَةِۭ
Open ayah 74:51Sun gudu daga zãki.
بَلۡ يُرِيدُ كُلُّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُمۡ أَن يُؤۡتَىٰ صُحُفٗا مُّنَشَّرَةٗ
Open ayah 74:52A'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa
كَلَّاۖ بَل لَّا يَخَافُونَ ٱلۡأٓخِرَةَ
Open ayah 74:53A'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira.
كَلَّآ إِنَّهُۥ تَذۡكِرَةٞ
Open ayah 74:54A'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce.
فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ
Open ayah 74:55Dõmin wanda ya so, ya tuna.
وَمَا يَذۡكُرُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُۚ هُوَ أَهۡلُ ٱلتَّقۡوَىٰ وَأَهۡلُ ٱلۡمَغۡفِرَةِ
Open ayah 74:56Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara.