المرسلات
Al-Mursalaat
Translation: Hausa - Abubakar Mahmoud Gumi · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلۡمُرۡسَلَٰتِ عُرۡفٗا
Open ayah 77:1Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.
فَٱلۡعَٰصِفَٰتِ عَصۡفٗا
Open ayah 77:2Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.
وَٱلنَّٰشِرَٰتِ نَشۡرٗا
Open ayah 77:3Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.
فَٱلۡفَٰرِقَٰتِ فَرۡقٗا
Open ayah 77:4sa'an nan, da ãyõyi mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.
فَٱلۡمُلۡقِيَٰتِ ذِكۡرًا
Open ayah 77:5Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.
عُذۡرًا أَوۡ نُذۡرًا
Open ayah 77:6Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi.
إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَٰقِعٞ
Open ayah 77:7Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne
فَإِذَا ٱلنُّجُومُ طُمِسَتۡ
Open ayah 77:8To, idan taurãri aka shãfe haskensu.
وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ فُرِجَتۡ
Open ayah 77:9Kuma, idan sama aka tsãge ta.
وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ نُسِفَتۡ
Open ayah 77:10Kuma, idan duwãtsu aka nike su.
وَإِذَا ٱلرُّسُلُ أُقِّتَتۡ
Open ayah 77:11Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.
لِأَيِّ يَوۡمٍ أُجِّلَتۡ
Open ayah 77:12Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali.
لِيَوۡمِ ٱلۡفَصۡلِ
Open ayah 77:13Domin rãnar rarrabẽwa.
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِ
Open ayah 77:14Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:15Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
أَلَمۡ نُهۡلِكِ ٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 77:16Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba.
ثُمَّ نُتۡبِعُهُمُ ٱلۡأٓخِرِينَ
Open ayah 77:17Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?
كَذَٰلِكَ نَفۡعَلُ بِٱلۡمُجۡرِمِينَ
Open ayah 77:18Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:19Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
أَلَمۡ نَخۡلُقكُّم مِّن مَّآءٖ مَّهِينٖ
Open ayah 77:20Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.
فَجَعَلۡنَٰهُ فِي قَرَارٖ مَّكِينٍ
Open ayah 77:21Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce.
إِلَىٰ قَدَرٖ مَّعۡلُومٖ
Open ayah 77:22Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna.
فَقَدَرۡنَا فَنِعۡمَ ٱلۡقَٰدِرُونَ
Open ayah 77:23Sa'an nan, Muka nũna iyãwarMu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa.
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:24Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
أَلَمۡ نَجۡعَلِ ٱلۡأَرۡضَ كِفَاتًا
Open ayah 77:25Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba.
أَحۡيَآءٗ وَأَمۡوَٰتٗا
Open ayah 77:26Ga rãyayyu da matattu,
وَجَعَلۡنَا فِيهَا رَوَٰسِيَ شَٰمِخَٰتٖ وَأَسۡقَيۡنَٰكُم مَّآءٗ فُرَاتٗا
Open ayah 77:27Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi?
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:28Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
ٱنطَلِقُوٓاْ إِلَىٰ مَا كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ
Open ayah 77:29Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi!
ٱنطَلِقُوٓاْ إِلَىٰ ظِلّٖ ذِي ثَلَٰثِ شُعَبٖ
Open ayah 77:30Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku.
لَّا ظَلِيلٖ وَلَا يُغۡنِي مِنَ ٱللَّهَبِ
Open ayah 77:31Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta.
إِنَّهَا تَرۡمِي بِشَرَرٖ كَٱلۡقَصۡرِ
Open ayah 77:32Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye.
كَأَنَّهُۥ جِمَٰلَتٞ صُفۡرٞ
Open ayah 77:33Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe.
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:34Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
هَٰذَا يَوۡمُ لَا يَنطِقُونَ
Open ayah 77:35Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba.
وَلَا يُؤۡذَنُ لَهُمۡ فَيَعۡتَذِرُونَ
Open ayah 77:36Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari.
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:37Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
هَٰذَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِۖ جَمَعۡنَٰكُمۡ وَٱلۡأَوَّلِينَ
Open ayah 77:38Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko.
فَإِن كَانَ لَكُمۡ كَيۡدٞ فَكِيدُونِ
Open ayah 77:39To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita.
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:40Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي ظِلَٰلٖ وَعُيُونٖ
Open ayah 77:41Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari.
وَفَوَٰكِهَ مِمَّا يَشۡتَهُونَ
Open ayah 77:42Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari.
كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ هَنِيٓـَٔۢا بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ
Open ayah 77:43(A ce musu) ";Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa.";
إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ
Open ayah 77:44Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:45Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
كُلُواْ وَتَمَتَّعُواْ قَلِيلًا إِنَّكُم مُّجۡرِمُونَ
Open ayah 77:46(Ana ce musu) ";Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne.";
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:47Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱرۡكَعُواْ لَا يَرۡكَعُونَ
Open ayah 77:48Kuma, idan an ce musu: ";Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba.";
وَيۡلٞ يَوۡمَئِذٖ لِّلۡمُكَذِّبِينَ
Open ayah 77:49Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
فَبِأَيِّ حَدِيثِۭ بَعۡدَهُۥ يُؤۡمِنُونَ
Open ayah 77:50To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni