النبإ
An-Naba
Translation: Hausa - Abubakar Mahmoud Gumi · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
عَمَّ يَتَسَآءَلُونَ
Open ayah 78:1A kan mẽ suke tambayar jũna?
عَنِ ٱلنَّبَإِ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 78:2A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)?
ٱلَّذِي هُمۡ فِيهِ مُخۡتَلِفُونَ
Open ayah 78:3Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa?
كَلَّا سَيَعۡلَمُونَ
Open ayah 78:4A'aha! Zã su sani.
ثُمَّ كَلَّا سَيَعۡلَمُونَ
Open ayah 78:5Kuma, a'aha! Zã su sani.
أَلَمۡ نَجۡعَلِ ٱلۡأَرۡضَ مِهَٰدٗا
Open ayah 78:6Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba?
وَٱلۡجِبَالَ أَوۡتَادٗا
Open ayah 78:7Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)?
وَخَلَقۡنَٰكُمۡ أَزۡوَٰجٗا
Open ayah 78:8Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã?
وَجَعَلۡنَا نَوۡمَكُمۡ سُبَاتٗا
Open ayah 78:9Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa?
وَجَعَلۡنَا ٱلَّيۡلَ لِبَاسٗا
Open ayah 78:10Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?
وَجَعَلۡنَا ٱلنَّهَارَ مَعَاشٗا
Open ayah 78:11Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci?
وَبَنَيۡنَا فَوۡقَكُمۡ سَبۡعٗا شِدَادٗا
Open ayah 78:12Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi?
وَجَعَلۡنَا سِرَاجٗا وَهَّاجٗا
Open ayah 78:13Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)?
وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلۡمُعۡصِرَٰتِ مَآءٗ ثَجَّاجٗا
Open ayah 78:14Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba?
لِّنُخۡرِجَ بِهِۦ حَبّٗا وَنَبَاتٗا
Open ayah 78:15Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi?
وَجَنَّٰتٍ أَلۡفَافًا
Open ayah 78:16Da itãcen lambuna mãsu lillibniya?
إِنَّ يَوۡمَ ٱلۡفَصۡلِ كَانَ مِيقَٰتٗا
Open ayah 78:17Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci.
يَوۡمَ يُنفَخُ فِي ٱلصُّورِ فَتَأۡتُونَ أَفۡوَاجٗا
Open ayah 78:18Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a.
وَفُتِحَتِ ٱلسَّمَآءُ فَكَانَتۡ أَبۡوَٰبٗا
Open ayah 78:19Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi.
وَسُيِّرَتِ ٱلۡجِبَالُ فَكَانَتۡ سَرَابًا
Open ayah 78:20Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra.
إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتۡ مِرۡصَادٗا
Open ayah 78:21Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata.
لِّلطَّٰغِينَ مَـَٔابٗا
Open ayah 78:22Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma.
لَّٰبِثِينَ فِيهَآ أَحۡقَابٗا
Open ayah 78:23Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna.
لَّا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرۡدٗا وَلَا شَرَابًا
Open ayah 78:24Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha.
إِلَّا حَمِيمٗا وَغَسَّاقٗا
Open ayah 78:25Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini.
جَزَآءٗ وِفَاقًا
Open ayah 78:26Sakamako mai dãcẽwa.
إِنَّهُمۡ كَانُواْ لَا يَرۡجُونَ حِسَابٗا
Open ayah 78:27Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi.
وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا كِذَّابٗا
Open ayah 78:28Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyinMu, ƙaryatãwa!
وَكُلَّ شَيۡءٍ أَحۡصَيۡنَٰهُ كِتَٰبٗا
Open ayah 78:29Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce.
فَذُوقُواْ فَلَن نَّزِيدَكُمۡ إِلَّا عَذَابًا
Open ayah 78:30Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba.
إِنَّ لِلۡمُتَّقِينَ مَفَازًا
Open ayah 78:31Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo.
حَدَآئِقَ وَأَعۡنَٰبٗا
Open ayah 78:32Lambuna da inabõbi.
وَكَوَاعِبَ أَتۡرَابٗا
Open ayah 78:33Da cikakkun 'yammata, tsãrar jũna.
وَكَأۡسٗا دِهَاقٗا
Open ayah 78:34Da hinjãlan giya cikakku.
لَّا يَسۡمَعُونَ فِيهَا لَغۡوٗا وَلَا كِذَّٰبٗا
Open ayah 78:35Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.
جَزَآءٗ مِّن رَّبِّكَ عَطَآءً حِسَابٗا
Open ayah 78:36Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa.
رَّبِّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا ٱلرَّحۡمَٰنِۖ لَا يَمۡلِكُونَ مِنۡهُ خِطَابٗا
Open ayah 78:37Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.
يَوۡمَ يَقُومُ ٱلرُّوحُ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ صَفّٗاۖ لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنۡ أَذِنَ لَهُ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَقَالَ صَوَابٗا
Open ayah 78:38Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.
ذَٰلِكَ ٱلۡيَوۡمُ ٱلۡحَقُّۖ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ مَـَٔابًا
Open ayah 78:39Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.
إِنَّآ أَنذَرۡنَٰكُمۡ عَذَابٗا قَرِيبٗا يَوۡمَ يَنظُرُ ٱلۡمَرۡءُ مَا قَدَّمَتۡ يَدَاهُ وَيَقُولُ ٱلۡكَافِرُ يَٰلَيۡتَنِي كُنتُ تُرَٰبَۢا
Open ayah 78:40Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: ";Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!";