الحاقة
Al-Haaqqa
Translation: Hausa - Abubakar Mahmoud Gumi · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
ٱلۡحَآقَّةُ
Open ayah 69:1Kiran gaskiya!
مَا ٱلۡحَآقَّةُ
Open ayah 69:2Mẽne ne kiran gaskiya?
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡحَآقَّةُ
Open ayah 69:3Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya?
كَذَّبَتۡ ثَمُودُ وَعَادُۢ بِٱلۡقَارِعَةِ
Open ayah 69:4Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya!
فَأَمَّا ثَمُودُ فَأُهۡلِكُواْ بِٱلطَّاغِيَةِ
Open ayah 69:5To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani.
وَأَمَّا عَادٞ فَأُهۡلِكُواْ بِرِيحٖ صَرۡصَرٍ عَاتِيَةٖ
Open ayah 69:6Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi.
سَخَّرَهَا عَلَيۡهِمۡ سَبۡعَ لَيَالٖ وَثَمَٰنِيَةَ أَيَّامٍ حُسُومٗاۖ فَتَرَى ٱلۡقَوۡمَ فِيهَا صَرۡعَىٰ كَأَنَّهُمۡ أَعۡجَازُ نَخۡلٍ خَاوِيَةٖ
Open ayah 69:7(Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi.
فَهَلۡ تَرَىٰ لَهُم مِّنۢ بَاقِيَةٖ
Open ayah 69:8To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu?
وَجَآءَ فِرۡعَوۡنُ وَمَن قَبۡلَهُۥ وَٱلۡمُؤۡتَفِكَٰتُ بِٱلۡخَاطِئَةِ
Open ayah 69:9Kuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi.
فَعَصَوۡاْ رَسُولَ رَبِّهِمۡ فَأَخَذَهُمۡ أَخۡذَةٗ رَّابِيَةً
Open ayah 69:10Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani).
إِنَّا لَمَّا طَغَا ٱلۡمَآءُ حَمَلۡنَٰكُمۡ فِي ٱلۡجَارِيَةِ
Open ayah 69:11Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan.
لِنَجۡعَلَهَا لَكُمۡ تَذۡكِرَةٗ وَتَعِيَهَآ أُذُنٞ وَٰعِيَةٞ
Open ayah 69:12Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi).
فَإِذَا نُفِخَ فِي ٱلصُّورِ نَفۡخَةٞ وَٰحِدَةٞ
Open ayah 69:13To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya.
وَحُمِلَتِ ٱلۡأَرۡضُ وَٱلۡجِبَالُ فَدُكَّتَا دَكَّةٗ وَٰحِدَةٗ
Open ayah 69:14Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya.
فَيَوۡمَئِذٖ وَقَعَتِ ٱلۡوَاقِعَةُ
Open ayah 69:15A ran nan, mai aukuwa zã ta auku.
وَٱنشَقَّتِ ٱلسَّمَآءُ فَهِيَ يَوۡمَئِذٖ وَاهِيَةٞ
Open ayah 69:16Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce.
وَٱلۡمَلَكُ عَلَىٰٓ أَرۡجَآئِهَاۚ وَيَحۡمِلُ عَرۡشَ رَبِّكَ فَوۡقَهُمۡ يَوۡمَئِذٖ ثَمَٰنِيَةٞ
Open ayah 69:17Kuma malã'iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã'iku) takwas na ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar.
يَوۡمَئِذٖ تُعۡرَضُونَ لَا تَخۡفَىٰ مِنكُمۡ خَافِيَةٞ
Open ayah 69:18A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa.
فَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ فَيَقُولُ هَآؤُمُ ٱقۡرَءُواْ كِتَٰبِيَهۡ
Open ayah 69:19To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), ";Ku karɓa, ku karanta littafina.";
إِنِّي ظَنَنتُ أَنِّي مُلَٰقٍ حِسَابِيَهۡ
Open ayah 69:20";Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne.";
فَهُوَ فِي عِيشَةٖ رَّاضِيَةٖ
Open ayah 69:21Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda.
فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٖ
Open ayah 69:22A cikin Aljanna maɗaukakiya.
قُطُوفُهَا دَانِيَةٞ
Open ayah 69:23Nunannun 'yã'yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba),
كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ هَنِيٓـَٔۢا بِمَآ أَسۡلَفۡتُمۡ فِي ٱلۡأَيَّامِ ٱلۡخَالِيَةِ
Open ayah 69:24(Ana ce musu) ";Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige.";
وَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِشِمَالِهِۦ فَيَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي لَمۡ أُوتَ كِتَٰبِيَهۡ
Open ayah 69:25Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: ";Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba!";
وَلَمۡ أَدۡرِ مَا حِسَابِيَهۡ
Open ayah 69:26";Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba!";
يَٰلَيۡتَهَا كَانَتِ ٱلۡقَاضِيَةَ
Open ayah 69:27";In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce!
مَآ أَغۡنَىٰ عَنِّي مَالِيَهۡۜ
Open ayah 69:28";Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba!";
هَلَكَ عَنِّي سُلۡطَٰنِيَهۡ
Open ayah 69:29";Ĩkona ya ɓace mini!";
خُذُوهُ فَغُلُّوهُ
Open ayah 69:30(Sai a ce wa malã'iku) ";Ku kãmã shi, sa'an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi.";
ثُمَّ ٱلۡجَحِيمَ صَلُّوهُ
Open ayah 69:31";Sa'an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi.";
ثُمَّ فِي سِلۡسِلَةٖ ذَرۡعُهَا سَبۡعُونَ ذِرَاعٗا فَٱسۡلُكُوهُ
Open ayah 69:32";Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã'i saba'in, sai ku sanya shi.";
إِنَّهُۥ كَانَ لَا يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 69:33";Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma!";
وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلۡمِسۡكِينِ
Open ayah 69:34";Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci!";
فَلَيۡسَ لَهُ ٱلۡيَوۡمَ هَٰهُنَا حَمِيمٞ
Open ayah 69:35";Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi.";
وَلَا طَعَامٌ إِلَّا مِنۡ غِسۡلِينٖ
Open ayah 69:36";Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn.";
لَّا يَأۡكُلُهُۥٓ إِلَّا ٱلۡخَٰطِـُٔونَ
Open ayah 69:37";Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci.";
فَلَآ أُقۡسِمُ بِمَا تُبۡصِرُونَ
Open ayah 69:38To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba,
وَمَا لَا تُبۡصِرُونَ
Open ayah 69:39Da abin da bã ku iya gani.
إِنَّهُۥ لَقَوۡلُ رَسُولٖ كَرِيمٖ
Open ayah 69:40Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne.
وَمَا هُوَ بِقَوۡلِ شَاعِرٖۚ قَلِيلٗا مَّا تُؤۡمِنُونَ
Open ayah 69:41Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata.
وَلَا بِقَوۡلِ كَاهِنٖۚ قَلِيلٗا مَّا تَذَكَّرُونَ
Open ayah 69:42Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa.
تَنزِيلٞ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 69:43Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka.
وَلَوۡ تَقَوَّلَ عَلَيۡنَا بَعۡضَ ٱلۡأَقَاوِيلِ
Open ayah 69:44Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu.
لَأَخَذۡنَا مِنۡهُ بِٱلۡيَمِينِ
Open ayah 69:45Dã Mun kãma shi da dãma.
ثُمَّ لَقَطَعۡنَا مِنۡهُ ٱلۡوَتِينَ
Open ayah 69:46sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã.
فَمَا مِنكُم مِّنۡ أَحَدٍ عَنۡهُ حَٰجِزِينَ
Open ayah 69:47Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbarMu) daga gare shi.
وَإِنَّهُۥ لَتَذۡكِرَةٞ لِّلۡمُتَّقِينَ
Open ayah 69:48Kuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa.
وَإِنَّا لَنَعۡلَمُ أَنَّ مِنكُم مُّكَذِّبِينَ
Open ayah 69:49Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa.
وَإِنَّهُۥ لَحَسۡرَةٌ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ
Open ayah 69:50Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai.
وَإِنَّهُۥ لَحَقُّ ٱلۡيَقِينِ
Open ayah 69:51Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙshẽni.
فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ
Open ayah 69:52Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma.