عبس
Abasa
Translation: Hausa - Abubakar Mahmoud Gumi · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
عَبَسَ وَتَوَلَّىٰٓ
Open ayah 80:1Yã game huska kuma ya jũya bãya.
أَن جَآءَهُ ٱلۡأَعۡمَىٰ
Open ayah 80:2Sabõda makãho yã je masa.
وَمَا يُدۡرِيكَ لَعَلَّهُۥ يَزَّكَّىٰٓ
Open ayah 80:3To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka.
أَوۡ يَذَّكَّرُ فَتَنفَعَهُ ٱلذِّكۡرَىٰٓ
Open ayah 80:4Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi?
أَمَّا مَنِ ٱسۡتَغۡنَىٰ
Open ayah 80:5Amma wanda ya wadãtu da dũkiya.
فَأَنتَ لَهُۥ تَصَدَّىٰ
Open ayah 80:6Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi!
وَمَا عَلَيۡكَ أَلَّا يَزَّكَّىٰ
Open ayah 80:7To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba?
وَأَمَّا مَن جَآءَكَ يَسۡعَىٰ
Open ayah 80:8Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa.
وَهُوَ يَخۡشَىٰ
Open ayah 80:9Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah.
فَأَنتَ عَنۡهُ تَلَهَّىٰ
Open ayah 80:10Kai kuma kã shagala ga barinsa!
كَلَّآ إِنَّهَا تَذۡكِرَةٞ
Open ayah 80:11A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce.
فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ
Open ayah 80:12Sabõda wanda ya so ya tunaShi (Allah).
فِي صُحُفٖ مُّكَرَّمَةٖ
Open ayah 80:13(Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa,
مَّرۡفُوعَةٖ مُّطَهَّرَةِۭ
Open ayah 80:14Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa.
بِأَيۡدِي سَفَرَةٖ
Open ayah 80:15A cikin hannãyen mala'iku marubũta.
كِرَامِۭ بَرَرَةٖ
Open ayah 80:16Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah.
قُتِلَ ٱلۡإِنسَٰنُ مَآ أَكۡفَرَهُۥ
Open ayah 80:17An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa!
مِنۡ أَيِّ شَيۡءٍ خَلَقَهُۥ
Open ayah 80:18Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi?
مِن نُّطۡفَةٍ خَلَقَهُۥ فَقَدَّرَهُۥ
Open ayah 80:19Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye).
ثُمَّ ٱلسَّبِيلَ يَسَّرَهُۥ
Open ayah 80:20Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa.
ثُمَّ أَمَاتَهُۥ فَأَقۡبَرَهُۥ
Open ayah 80:21Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari.
ثُمَّ إِذَا شَآءَ أَنشَرَهُۥ
Open ayah 80:22Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi.
كَلَّا لَمَّا يَقۡضِ مَآ أَمَرَهُۥ
Open ayah 80:23Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari).
فَلۡيَنظُرِ ٱلۡإِنسَٰنُ إِلَىٰ طَعَامِهِۦٓ
Open ayah 80:24To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa.
أَنَّا صَبَبۡنَا ٱلۡمَآءَ صَبّٗا
Open ayah 80:25Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa.
ثُمَّ شَقَقۡنَا ٱلۡأَرۡضَ شَقّٗا
Open ayah 80:26Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa.
فَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا حَبّٗا
Open ayah 80:27Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta.
وَعِنَبٗا وَقَضۡبٗا
Open ayah 80:28Da inabi da ciyãwa.
وَزَيۡتُونٗا وَنَخۡلٗا
Open ayah 80:29Da zaitũni da itãcen dabĩno.
وَحَدَآئِقَ غُلۡبٗا
Open ayah 80:30Da lambuna, mãsu yawan itãce.
وَفَٰكِهَةٗ وَأَبّٗا
Open ayah 80:31Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi.
مَّتَٰعٗا لَّكُمۡ وَلِأَنۡعَٰمِكُمۡ
Open ayah 80:32Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku.
فَإِذَا جَآءَتِ ٱلصَّآخَّةُ
Open ayah 80:33To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo.
يَوۡمَ يَفِرُّ ٱلۡمَرۡءُ مِنۡ أَخِيهِ
Open ayah 80:34Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa.
وَأُمِّهِۦ وَأَبِيهِ
Open ayah 80:35Da uwarsa da ubansa.
وَصَٰحِبَتِهِۦ وَبَنِيهِ
Open ayah 80:36Da mãtarsa da ɗiyansa.
لِكُلِّ ٱمۡرِيٕٖ مِّنۡهُمۡ يَوۡمَئِذٖ شَأۡنٞ يُغۡنِيهِ
Open ayah 80:37Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi.
وُجُوهٞ يَوۡمَئِذٖ مُّسۡفِرَةٞ
Open ayah 80:38Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne.
ضَاحِكَةٞ مُّسۡتَبۡشِرَةٞ
Open ayah 80:39Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra.
وَوُجُوهٞ يَوۡمَئِذٍ عَلَيۡهَا غَبَرَةٞ
Open ayah 80:40Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu.
تَرۡهَقُهَا قَتَرَةٌ
Open ayah 80:41Baƙi zai rufe su.
أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَفَرَةُ ٱلۡفَجَرَةُ
Open ayah 80:42Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu).