التكوير
At-Takwir
Translation: Hausa - Abubakar Mahmoud Gumi · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
إِذَا ٱلشَّمۡسُ كُوِّرَتۡ
Open ayah 81:1Idan rãna aka shafe haskenta
وَإِذَا ٱلنُّجُومُ ٱنكَدَرَتۡ
Open ayah 81:2Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani).
وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ سُيِّرَتۡ
Open ayah 81:3Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su.
وَإِذَا ٱلۡعِشَارُ عُطِّلَتۡ
Open ayah 81:4Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba.
وَإِذَا ٱلۡوُحُوشُ حُشِرَتۡ
Open ayah 81:5Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su.
وَإِذَا ٱلۡبِحَارُ سُجِّرَتۡ
Open ayah 81:6Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta.
وَإِذَا ٱلنُّفُوسُ زُوِّجَتۡ
Open ayah 81:7Kuma idan rãyuka aka haɗa su da jikunkunansu.
وَإِذَا ٱلۡمَوۡءُۥدَةُ سُئِلَتۡ
Open ayah 81:8Kuma idan wadda aka turbuɗe ta da rai aka tambaye ta.
بِأَيِّ ذَنۢبٖ قُتِلَتۡ
Open ayah 81:9";Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?";
وَإِذَا ٱلصُّحُفُ نُشِرَتۡ
Open ayah 81:10Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su).
وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ كُشِطَتۡ
Open ayah 81:11Kuma idan sama aka fẽɗe ta.
وَإِذَا ٱلۡجَحِيمُ سُعِّرَتۡ
Open ayah 81:12Kuma idan Jahĩm aka hũra ta
وَإِذَا ٱلۡجَنَّةُ أُزۡلِفَتۡ
Open ayah 81:13Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita.
عَلِمَتۡ نَفۡسٞ مَّآ أَحۡضَرَتۡ
Open ayah 81:14Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan).
فَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلۡخُنَّسِ
Open ayah 81:15To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã ba.
ٱلۡجَوَارِ ٱلۡكُنَّسِ
Open ayah 81:16Mãsu gudu suna ɓũya.
وَٱلَّيۡلِ إِذَا عَسۡعَسَ
Open ayah 81:17Da dare idan ya bãyar da bãya.
وَٱلصُّبۡحِ إِذَا تَنَفَّسَ
Open ayah 81:18Da sãfiya idan ta yi lumfashi.
إِنَّهُۥ لَقَوۡلُ رَسُولٖ كَرِيمٖ
Open ayah 81:19Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah.
ذِي قُوَّةٍ عِندَ ذِي ٱلۡعَرۡشِ مَكِينٖ
Open ayah 81:20Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi.
مُّطَاعٖ ثَمَّ أَمِينٖ
Open ayah 81:21Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce.
وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجۡنُونٖ
Open ayah 81:22Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne.
وَلَقَدۡ رَءَاهُ بِٱلۡأُفُقِ ٱلۡمُبِينِ
Open ayah 81:23Kuma lalle ne, yã gan shi a cikin sararin sama mabayyani.
وَمَا هُوَ عَلَى ٱلۡغَيۡبِ بِضَنِينٖ
Open ayah 81:24Kuma shi, ga gaibi bã mai rowa ba ne.
وَمَا هُوَ بِقَوۡلِ شَيۡطَٰنٖ رَّجِيمٖ
Open ayah 81:25Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce.
فَأَيۡنَ تَذۡهَبُونَ
Open ayah 81:26Shin, a inã zã ku tafi?
إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرٞ لِّلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 81:27Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai.
لِمَن شَآءَ مِنكُمۡ أَن يَسۡتَقِيمَ
Open ayah 81:28Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu.
وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ
Open ayah 81:29Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda.