الإنفطار
Al-Infitaar
Translation: Hausa - Abubakar Mahmoud Gumi · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنفَطَرَتۡ
Open ayah 82:1Idan sama ta tsãge.
وَإِذَا ٱلۡكَوَاكِبُ ٱنتَثَرَتۡ
Open ayah 82:2Kuma idan taurãri suka wãtse.
وَإِذَا ٱلۡبِحَارُ فُجِّرَتۡ
Open ayah 82:3Kuma idan tẽkuna aka facce su.
وَإِذَا ٱلۡقُبُورُ بُعۡثِرَتۡ
Open ayah 82:4Kuma idan kaburbura aka tõne su.
عَلِمَتۡ نَفۡسٞ مَّا قَدَّمَتۡ وَأَخَّرَتۡ
Open ayah 82:5Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.
يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡإِنسَٰنُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ ٱلۡكَرِيمِ
Open ayah 82:6Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci.
ٱلَّذِي خَلَقَكَ فَسَوَّىٰكَ فَعَدَلَكَ
Open ayah 82:7Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.
فِيٓ أَيِّ صُورَةٖ مَّا شَآءَ رَكَّبَكَ
Open ayah 82:8A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.
كَلَّا بَلۡ تُكَذِّبُونَ بِٱلدِّينِ
Open ayah 82:9A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!
وَإِنَّ عَلَيۡكُمۡ لَحَٰفِظِينَ
Open ayah 82:10Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.
كِرَامٗا كَٰتِبِينَ
Open ayah 82:11Mãsu daraja, marubũta.
يَعۡلَمُونَ مَا تَفۡعَلُونَ
Open ayah 82:12Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.
إِنَّ ٱلۡأَبۡرَارَ لَفِي نَعِيمٖ
Open ayah 82:13Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.
وَإِنَّ ٱلۡفُجَّارَ لَفِي جَحِيمٖ
Open ayah 82:14Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.
يَصۡلَوۡنَهَا يَوۡمَ ٱلدِّينِ
Open ayah 82:15Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.
وَمَا هُمۡ عَنۡهَا بِغَآئِبِينَ
Open ayah 82:16Bã zã su faku daga gare ta ba.
وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلدِّينِ
Open ayah 82:17Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako?
ثُمَّ مَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلدِّينِ
Open ayah 82:18Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?
يَوۡمَ لَا تَمۡلِكُ نَفۡسٞ لِّنَفۡسٖ شَيۡـٔٗاۖ وَٱلۡأَمۡرُ يَوۡمَئِذٖ لِّلَّهِ
Open ayah 82:19Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.