البروج
Al-Burooj
Translation: Hausa - Abubakar Mahmoud Gumi · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلۡبُرُوجِ
Open ayah 85:1Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara.
وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡمَوۡعُودِ
Open ayah 85:2Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa,
وَشَاهِدٖ وَمَشۡهُودٖ
Open ayah 85:3Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta a cikinsa
قُتِلَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡأُخۡدُودِ
Open ayah 85:4An la'ani mutãnen rãmi.
ٱلنَّارِ ذَاتِ ٱلۡوَقُودِ
Open ayah 85:5Wato wuta wadda aka hura.
إِذۡ هُمۡ عَلَيۡهَا قُعُودٞ
Open ayah 85:6A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune.
وَهُمۡ عَلَىٰ مَا يَفۡعَلُونَ بِٱلۡمُؤۡمِنِينَ شُهُودٞ
Open ayah 85:7Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce.
وَمَا نَقَمُواْ مِنۡهُمۡ إِلَّآ أَن يُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَمِيدِ
Open ayah 85:8Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa.
ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٖ شَهِيدٌ
Open ayah 85:9Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake.
إِنَّ ٱلَّذِينَ فَتَنُواْ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ ثُمَّ لَمۡ يَتُوبُواْ فَلَهُمۡ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَلَهُمۡ عَذَابُ ٱلۡحَرِيقِ
Open ayah 85:10Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara.
إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُمۡ جَنَّٰتٞ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡكَبِيرُ
Open ayah 85:11Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba.
إِنَّ بَطۡشَ رَبِّكَ لَشَدِيدٌ
Open ayah 85:12Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai.
إِنَّهُۥ هُوَ يُبۡدِئُ وَيُعِيدُ
Open ayah 85:13Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa).
وَهُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلۡوَدُودُ
Open ayah 85:14Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya.
ذُو ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡمَجِيدُ
Open ayah 85:15Mai Al'arshi mai girma
فَعَّالٞ لِّمَا يُرِيدُ
Open ayah 85:16Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi.
هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلۡجُنُودِ
Open ayah 85:17Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka.
فِرۡعَوۡنَ وَثَمُودَ
Open ayah 85:18Fir'auna da samũdãwa?
بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فِي تَكۡذِيبٖ
Open ayah 85:19Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa.
وَٱللَّهُ مِن وَرَآئِهِم مُّحِيطُۢ
Open ayah 85:20Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da saninSa).
بَلۡ هُوَ قُرۡءَانٞ مَّجِيدٞ
Open ayah 85:21Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma.
فِي لَوۡحٖ مَّحۡفُوظِۭ
Open ayah 85:22A cikin Allo tsararre.