الشرح
Ash-Sharh
Translation: Hausa - Abubakar Mahmoud Gumi · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
أَلَمۡ نَشۡرَحۡ لَكَ صَدۡرَكَ
Open ayah 94:1Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)?
وَوَضَعۡنَا عَنكَ وِزۡرَكَ
Open ayah 94:2Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe.
ٱلَّذِيٓ أَنقَضَ ظَهۡرَكَ
Open ayah 94:3Wanda ya nauyayi bãyanka?
وَرَفَعۡنَا لَكَ ذِكۡرَكَ
Open ayah 94:4Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka?
فَإِنَّ مَعَ ٱلۡعُسۡرِ يُسۡرًا
Open ayah 94:5To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
إِنَّ مَعَ ٱلۡعُسۡرِ يُسۡرٗا
Open ayah 94:6Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi.
فَإِذَا فَرَغۡتَ فَٱنصَبۡ
Open ayah 94:7Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah).
وَإِلَىٰ رَبِّكَ فَٱرۡغَب
Open ayah 94:8Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi.