الضحى
Ad-Dhuhaa
Translation: Hausa - Abubakar Mahmoud Gumi · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلضُّحَىٰ
Open ayah 93:1Inã rantsuwa da hantsi.
وَٱلَّيۡلِ إِذَا سَجَىٰ
Open ayah 93:2Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa).
مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَىٰ
Open ayah 93:3Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba.
وَلَلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٞ لَّكَ مِنَ ٱلۡأُولَىٰ
Open ayah 93:4Kuma lalle ta ƙarshe ce mafi alheri a gare ka daga ta farko.
وَلَسَوۡفَ يُعۡطِيكَ رَبُّكَ فَتَرۡضَىٰٓ
Open ayah 93:5Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda.
أَلَمۡ يَجِدۡكَ يَتِيمٗا فَـَٔاوَىٰ
Open ayah 93:6Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma?
وَوَجَدَكَ ضَآلّٗا فَهَدَىٰ
Open ayah 93:7Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai?
وَوَجَدَكَ عَآئِلٗا فَأَغۡنَىٰ
Open ayah 93:8Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka?
فَأَمَّا ٱلۡيَتِيمَ فَلَا تَقۡهَرۡ
Open ayah 93:9Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi.
وَأَمَّا ٱلسَّآئِلَ فَلَا تَنۡهَرۡ
Open ayah 93:10Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa.
وَأَمَّا بِنِعۡمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثۡ
Open ayah 93:11Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya).