التكاثر
At-Takaathur
Translation: Hausa - Abubakar Mahmoud Gumi · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
أَلۡهَىٰكُمُ ٱلتَّكَاثُرُ
Open ayah 102:1Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (dagaibada mai amfaninku).
حَتَّىٰ زُرۡتُمُ ٱلۡمَقَابِرَ
Open ayah 102:2Har kuka ziyarci kaburbura.
كَلَّا سَوۡفَ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 102:3A'aha! (Nan gaba) zã ku sani.
ثُمَّ كَلَّا سَوۡفَ تَعۡلَمُونَ
Open ayah 102:4Sa'an nan, tabbas, zã ku sani.
كَلَّا لَوۡ تَعۡلَمُونَ عِلۡمَ ٱلۡيَقِينِ
Open ayah 102:5Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni.
لَتَرَوُنَّ ٱلۡجَحِيمَ
Open ayah 102:6Lalle ne da kuna ganin Jahĩm.
ثُمَّ لَتَرَوُنَّهَا عَيۡنَ ٱلۡيَقِينِ
Open ayah 102:7Sa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane.
ثُمَّ لَتُسۡـَٔلُنَّ يَوۡمَئِذٍ عَنِ ٱلنَّعِيمِ
Open ayah 102:8Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku).