العلق
Al-Alaq
Translation: Hausa - Abubakar Mahmoud Gumi · Open the surah
بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
ٱقۡرَأۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلَّذِي خَلَقَ
Open ayah 96:1Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta.
خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ مِنۡ عَلَقٍ
Open ayah 96:2Ya hahitta mutum daga gudan jini.
ٱقۡرَأۡ وَرَبُّكَ ٱلۡأَكۡرَمُ
Open ayah 96:3Ka yi karatu, kuma UbangiJinka shi ne Mafi karimci.
ٱلَّذِي عَلَّمَ بِٱلۡقَلَمِ
Open ayah 96:4Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami.
عَلَّمَ ٱلۡإِنسَٰنَ مَا لَمۡ يَعۡلَمۡ
Open ayah 96:5Ya sanar da mutum abin da bai sani ba.
كَلَّآ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَيَطۡغَىٰٓ
Open ayah 96:6A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu).
أَن رَّءَاهُ ٱسۡتَغۡنَىٰٓ
Open ayah 96:7Dõmin yã ga kansa, yã wadãta.
إِنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلرُّجۡعَىٰٓ
Open ayah 96:8Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take.
أَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي يَنۡهَىٰ
Open ayah 96:9Shin, kã ga wanda ke hana.
عَبۡدًا إِذَا صَلَّىٰٓ
Open ayah 96:10Bãwã idan yã yi salla?
أَرَءَيۡتَ إِن كَانَ عَلَى ٱلۡهُدَىٰٓ
Open ayah 96:11Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya?
أَوۡ أَمَرَ بِٱلتَّقۡوَىٰٓ
Open ayah 96:12Ko ya yi umurni da taƙawa?
أَرَءَيۡتَ إِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰٓ
Open ayah 96:13Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya?
أَلَمۡ يَعۡلَم بِأَنَّ ٱللَّهَ يَرَىٰ
Open ayah 96:14Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani?
كَلَّا لَئِن لَّمۡ يَنتَهِ لَنَسۡفَعَۢا بِٱلنَّاصِيَةِ
Open ayah 96:15A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa.
نَاصِيَةٖ كَٰذِبَةٍ خَاطِئَةٖ
Open ayah 96:16Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi.
فَلۡيَدۡعُ نَادِيَهُۥ
Open ayah 96:17Sai ya kirayi ƙungiyarsa.
سَنَدۡعُ ٱلزَّبَانِيَةَ
Open ayah 96:18Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma).
كَلَّا لَا تُطِعۡهُ وَٱسۡجُدۡۤ وَٱقۡتَرِب۩
Open ayah 96:19A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u, kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka).